"Ban Taba Cewa Zan Rushe Masarautun Kano Ba" – Zababben Gwamnan Jihar Kano

"Ban Taba Cewa Zan Rushe Masarautun Kano Ba" – Zababben Gwamnan Jihar Kano

  • Zabben gwamnan jihar Kano, Abba Kabir ya magantu a kan rade-radin cewa yana shirin rushe masarautun Kano da gwamnatin Ganduje ta kirkiro
  • Abba Gida-Gida ya ce wannan magana duk shaci fadi ne babu kamshin gaskiya a cikinta
  • Ya ce gwamnatinsa ba za ta yi abun da baya bisa ka'ida ba amma dai za ta binciki duk masu guntun kashi a tsuliyarsu

Kano - Zababben gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf wanda aka fi sani da Abba Gida-gida ya karyata rade-radin da ake yi na cewar zai rushe wani gini ko masarautun jihar Kano da gwamnati mai ci ta kafa.

A wata hira da ya yi da shafin RFI a Facebook, Abba ya bayyana cewa tun da yake kamfen dinsa a fadin kananan hukumomi 44 na jihar ba a taba ji ya furta batun rushe gini ko korar sarakuna ba.

Kara karanta wannan

Abba Gida-gida: Sabon gwamnan Kano ya yi magana, ya fadi abin da ya shiryawa Kanawa

Zababben gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf
Ban Taba Cewa Zan Rushe Masarautun Kano Ba – Zababben Gwamnan Jihar Kano Hoto: The Cable
Asali: UGC

Ya bayyana cewa shi kadai dan takarar da idan ya ziyarci karamar hukuma idan har akwai sarki ciki sai ya kai masa ziyara ta musamman don girmamawa.

Za mu kafa kwamiti da zai duba bukatun jama'a a watanni ukun farko

Sai dai kuma, zababben gwamnan ya ce akwai wani zama na musamman da kwamitocin da za su kafa wanda zai duba bukatun al’ummar Jihar daba-daban cikin watanni uku na farko na gwamnatinsa. Ya ce da su ne za su yi aiki.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Abba ya ce:

“Gaskiyar lamari ni dai tun da na fara kamfen wato na zagaya kananan hukumomi 44 kuma ni kadai ne dan takara wanda ya zagaya kananan hukumomi 44 ya gabatar da manufofinsa ga al’ummar wadannan kananan hukumomi.
“Duk inda na je ina gabatar da manufofi wanda za su taimaki al’umma amma ba a taba ji na bude baki na ce zan rushe wani wuri ko kuma na ce zan kori wasu sarakuna ba.

Kara karanta wannan

Buri ya cika: Daga cin zabe, sabon gwamnan Sokotomya fadi abubuwa 9 da zai yi

“Hasalima ni kadai ne wanda duk karamar hukumar da na je idan sarki ne a wajen sai na je na kai masa ziyara, na gabatar masa da manufofi, idan kuma hakimi ne sai na je an tara min Dagatai da malamai na fada musu manufofina.
“Saboda haka shaci fadi ne kawai zancen, kuma ina tabbatar maka duk wadanda ka ji suna wannan cece-kucen, to suna da guntun kashi a tattare da su, mutane ne wadanda watakila su ne suka hada baki da azzalumai suka yi abinda bai kamata ba.
“Mu kuma gwamnatinmu duk wanda ya san cewa ya yi aiki daidai yana da gaskiya ta ya je ya hau gadonsa ya yi barci, babu abin da zai same shi.”

Za mu binciki barayin kudaden gwamnati - Abba gida-gida

Zababben gwamnan ya kuma bukaci duk wanda ya san ya hamdame kudaden jama'a da ya zama cikin shiri domin ba za su barsa ya ci bulus ba.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Gwamnatin Kano Ta Saka Dokar Hana FitaDaga Safe Har Dare

Ga bidiyon hirar a kasa:

A baya mun ji cewa zababben gwamnan na Kano ya yi alkawarin yin mulki daidai da bukatar al’umma da kuma kawo musu mafita ga matsalolinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng