Buhari Ya Yi Sabon Nadi Mai Muhimmanci Ana Daf Da Karewar Wa'adinsa A Watan Mayu

Buhari Ya Yi Sabon Nadi Mai Muhimmanci Ana Daf Da Karewar Wa'adinsa A Watan Mayu

  • Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya amince da sake nadin Idris Musa a matsayin babban daraktan NOSDRA
  • Hakan ya biyo bayan cikar wa'adin shekara hudu da ya yi inda aka nada shi a watan Afrilun 2019 tun da farko
  • Ma'aikatar Muhalli ce ta sanar da nadin a shafinta na Tuwita a ranar Litinin, tare da bayyana kwazon Musa a matsayin dalilin sake nada shi

FCT, Abuja - Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya amince da sake na Idris Musa a matsayin babban daraktan hukumar kiyaye kwarewar man fetur da kawo daukin gagagwa.

Ma'aikatar Muhalli ce ta sanar da hakan a shafinta na Tuwita (@FMEnvng) a ranar Litinin.

Idris
Buhari Ya Sake Nada Idris Musa A Matsayin Shugaban NOSDRA. Hoto: The Punch
Asali: Facebook

Sake nada shi na da alaka da irin kwazon aikinsa a shekaru hudu da suka wuce.

An nada Musa a karon farko ranar 1 ga watan Afrilu, 2019, na tsohon wa'adin shekara hudu.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Tsohuwa ta rude, ta kone danta, matarsa da jikokinta a wata jiha

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar sanarwar, sabon nadin zai fara aiki daga 1 ga watan Afrilu, 2023.

''Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da sabonta nadin Idris O Musa a matsayin babban daraktan NOSDRA karo na biyu kuma na karshe tsahon wa'adin shekara hudu.''
''Manyan dalilai sun hadar da zamantar da kundin bayanan hukumar, gyara duk wasu hanyoyin da za a bi don takaita kwararewar mai, da kuma duba taswiwar tabbatar da tsaftar muhalli.
''Ana amfani da taswirar a jihohin da ke samar da man fetur don kiyaye gurbacewar yanayi a yankin Niger Delta.
''Ya kuma gudanar ta tarukan wayar da kai game da illar basa bututun mai.
''Musa ya kuma kawo sauyi ta hanyar amfani da yanar gizo don samar da takardun bayanan kiyaye muhalli da kuma samar da na'aurar da za ta nuna ta inda iskar gas ko mai ya ke fita.

Kara karanta wannan

Azumin bana: Sarkin Musulmi ya fadi ranar da ya kamata a fara duban jinjirin wata

''Wannan kokarin na nuni da yadda ake komai a bayyane don kiyaye muhalli a masana'antar mai da iskar gas."

Sanarwar ta kara da cewa NOSDRA ta fara kokarin bibiyar methane, wata iska da ke kawo dumamar yanayi ga duniya ta kuma canja yanayi a wuraren da ke samar da man fetur a Najeriya.

''Hukumar ta fara shirye shiryen bibiyar iskar methane a jihohin da ke samar da man fetur a Najeriya'' in ji sanarwar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164