Wata Sabuwar Gobara Ta Tashi a Wata Babbar Kasuwar Jihar Anambra

Wata Sabuwar Gobara Ta Tashi a Wata Babbar Kasuwar Jihar Anambra

  • Wata mummunar gobara ta sake tashi a wata babbar kasuwar jihar Anambra a safiyar ranar Talata
  • Gobarar ta tashi ne da sanyin safiyar ranar Talata a ɓangaren masu siyar da kayan sanyawa na kasuwa
  • Gobarar wacce ba a san takaimaiman abinda ya haddasa sa ta ba ta janyo asarar miliyoyin naira

Jihar Anambra- Wata gobara ta tashi a ɓangaren White House na kasuwar Onitsha a cikin jihar Anambra.

Ɓangaren wanda aka fi sani da “Gbongboro”, yana a matsayin wajen adana kaya ne da kuma siyar da lesuka da sauran kayan sanyawa wanda yake a bayan kasuwar. Rahoton The Punch

Gobara
Wata Sabuwar Gobara Ta Tashi a Wata Babbar Kasuwar Jihar Anambra Hoto: Daily Post
Asali: UGC

Babu wanda zai iya bayar da takamaiman dalilin tashin gobarar ba wacce ta fara a safiyar ranar Talata inda ta laƙume kaya na miliyoyin nairori.

Ƴan kasuwar sun yi ta zagarabtu domin samun kwashe ƴan ragowar kayayyakin da basu kama da wutar ba, yayin da suka kira ƴan kwana-kwana. Rahoton Daily Post

Kara karanta wannan

Karin Bayani: 'Yan Bindiga Sun Kai Kazamin Harin Wurin Raba Kayayyakin Zabe, Sun Tafka Barna

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wani shaidar ganau ba jiyau ba ya bayyana cewa:

“Gobarar ta fara ne a ɓangaren White House inda suke siyar da kayan lesuka. Wajen yakamata ya kasance tashar mota ce da hanyar fita ta gaggawa amma mutane sun yi shaguna ba bisa ƙa'ida da amincewar wasu jami'an gwamnati a wajen."
"Ko da ƴan kwana-kwanan sun ƙaraso, da wuya a samu ta inda za su iya shiga wajen a sauƙaƙe domin ƙoƙarin kashe gobarar. Har su kan su ƴan kasuwar sun kasa shiga wajen su ɗauko kayayyakin su, wanda hakan ya sanya wutar ta cigaba da ci."

Ba a samu jin ta bakin shugaban hukumar kwana-kwana ta jihar, Martin Agbili, ba har ya zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton.

Gobara Ta Sake Tashi a Wasu Kasuwanni Biyu a Jihar Kano

A wani labarin na daban kuma, kun samu rahoto kan yadda wata gobara tansake tashi a wasu manyan kasuwanni biyu a jihar Kano.

Gobarar dai ta tashi ne a wata babbar kasuwar tumatiri a cikin jihar ta Kano inda ta janyo asarar dukiya mai tarin yawa. Sannan kuma wata gobarar ta tashi a inda aka siyar da kayan wayoyi a cikin wata ƙaramar hukuma a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng