Yanzu-Yanzu: An Sace Sakataren Jam'iyyar APC a jihar Rivers
- Ƴan bindiga sun kai farmaki jihar Rivers inda suka yi awon gaba da wani babban jigo kuma shugaba a jam'iyyar All Progressives Congress (APC)
- Ƴan bindigan dai sun je har gida sannan suka tafi da sakataren jam'iyyar APC na ƙaramar hukumar Ikwerre ta jihar
- Wani babban jigo a jam'iyyar APC ta jihar ya tabbatar da sace sakataren da ƴan bindigan suka yi
Jihar Rivers- Ƴan bindiga sun sace wani babban jigo kuma sakataren jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Mr Amadi Osaronu a ƙaramar hukumar Ikwerre ta jihar Rivers.
Ƴan bindigan sanye da kayan ƴan sanda sun je har gida sannan suka sace Osaronu a gidansa dake a Aluu, cikin ƙaramar hukumar Ikwerre, a ranar Laraba. Rahoton The Punch
Sakataren watsa labarai na jam'iyyar APC a jihar, Darlington Nwauju, shine ya tabbatar da aukuwar lamarin a ranar Alhamis.
Ana Dab Da Zabe, Burin Jam'iyyar Peter Obi Na Samun Gwamna Ya Samu Tawaya, Dubunnan Mambobin Jam'iyyar Sun Koma PDP
“Duk irin tsangwama da sanya tsoro a zukatan mutane da wata irin kitimurmura bata isa ta sauya shan kashin da jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) zata yi ba." A cewar sa
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƙarin bayani na nan tafe.....
Ana Daf Da Zabe, Makisa Sun Kai Wa Dan Takarar Gwamnan PDP Hari
A wani labarin na daban kuma, ɗan takarar gwamnan jihar Delta a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), ya sha da ƙyar a hannun ƴan bindiga.
Ƴan bindigan dai sun kai farmaki ga tawagar motocin ɗan takarar gwamnan, Hon Sheriff Oborevwori wanda shine shugaban majalisar dokokin jihar.
Asali: Legit.ng