Wata Mata Mai Shayarwa Ta Jefar Da Jinjirinta Yayin Tserewa Daga Yan Bindiga A Neja

Wata Mata Mai Shayarwa Ta Jefar Da Jinjirinta Yayin Tserewa Daga Yan Bindiga A Neja

  • Mamayar yan Sara-Suka a yankin Gbeganau da ke Jihar Niger ya janyo wata uwa ta cillar da jaririnta a gudun neman tsira
  • Al'ummar yankin sun bayyana irin fargabar da su ke shiga sakamakon harin yan tada kayar baya da ya addabi yankin
  • Hadin gwiwar jami'an sintiri da wata hukumar tsaro mai zaman kanta sun ceto yaron tare da mika shi asibiti wanda yanzu ya ke cikin koshin lafiya

Jihar Niger - Wata mata mai shayarwa ta gudu ta bar jaririnta yayin da ta ke gudarwa yan tada kayar baya, da aka fi sani da yan sara-suka, da suka mamaye unguwarsu a Minna, da ke Jihar Niger, rahoton Daily Trust.

Jaridar City & Crime ta ruwaito cewa lamarin ya faru ranar Alhamis a yankin Gbeganau lokacin da gungun yan tada kayar bayan suka kai farmaki yankin tare da balle shaguna.

Kara karanta wannan

“Kudi Da Nake Nema” Matashi Ya Yi Bidiyon Buhuhunan Tsoffin Kudi Da CBN Ya Nika Ya Watsar

Taswirar Neja
Mata mai shayarwa ta jefar da jijinrinta don tserewa yan bindiga a Niger. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Matar, wanda lamarin ya rutsa da ita, bata iya gudu sosai da jaririn a hannunta yayin da ta fadi a kasa ta kuma sake jaririn.

Jami'an tsaro sun ceto jinjirin

Shugaban kamfanin buga bulo da ke yankin, Mallam Abdullahi Ibrahim, ya shaidawa wakilin majiyarmu cewa sai da aka yi hadin gwiwa tsakanin jami'an sintiri da kuma jami'an yaki da miyagun kwayoyi - wani kamfanin bayar da tsaro mai zaman kansa - kafin ceto jaririn da kuma kai shi asibiti.

Ya ce:

''Kafin yanzu, yankin mu ya shawara a bangaren zaman lafiya. Amma yanzu babu kwanciyar hankali. Tsahon kwanaki biyu yanzu bama iya bacci.
''Wata mata tana gudu saboda yaran da suka mamaye unguwar har sai da ta cillar da jaririn da ke rike a hannunta. Jami'an sintiri ne da kuma jami'an hana shan miyagun kwayoyi (Anti-Drug Corps) suka kawo mana dauki a wannan ranar. An kai jaririn asibiti kuma yanzu yana cikin koshin lafiya. Amma har yanzu muna cikin fargaba."

Kara karanta wannan

Sauya Naira: Manyan Arewa Sun Fada Wa Shugaba Buhari Abinda Zai Faru Idan Ya Ki Bin Umarnin Kotun Koli

Mazauna unguwa sun yi kira ga gwamnati ta kawo musu taimako

Ibrahim, wanda ya roki gwamnatin jihar da kuma jami'an tsaro da su kawo musu dauki, ya kara da cewa:

''Akwai lokacin da yaran nan suka shigo mana unguwa suka balle shaguna shida. Suka daki mai shago daya har suka ji masa rauni kafin su yi sata a shagonsa. Sai da aka kwantar da shi na kwana uku.''

Da ya ke jawabi, Dr Malik Abdulganiyu na Unguwan Zaka, Gbeganau, ya ce,

''Satin da ya gabata, wadannan yan tada kayar bayan sun yamutsa hazo a yankinmu. Sun shigo cikin dare da makamai. Abin takaici ne ace an kyale yaran nan suna cutar da mu.''

Zaka, ya yi kira ga iyaye da su gargadi yayansu akan su daina wannan mummunan aiki, yana mai cewa:

''iyaye ba za su ce ba su san halin da ake ciki ba, ya kuma yi kira ga gwamnati ta kirkiri sana'o'i da matasa za su dinga yi don rage zaman banza da harkar daba, yana mai cewa, a duk lokacin da suka fara, babu wanda su ke dagawa kafa, wanda hakan ke janyo asarar rayuka da dukiyoyi."

Kara karanta wannan

Ba ka dariya ne? Jama'a sun kadu bayan ganin hotunan Shettima lokacin da yake jami'a

A wani rahoton kun ji cewa wasu yan bindiga sun yi awon gaba da mutane a kalla 50 a wasu kauyuka na jihar Niger inda suka sace kayayyakinsu masu daraja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164