"Na tsallaka Teku Da Hamadar Sahara Don Tserewa Daga Kasar, Babu Tabbass a Najeriya" - Matashi

"Na tsallaka Teku Da Hamadar Sahara Don Tserewa Daga Kasar, Babu Tabbass a Najeriya" - Matashi

  • Wani dan Najeriya da zama a kasar Italiya ya yi karin haske kan hanyar da ya bi wajen komawa Turai da zama
  • A cewar mutumin, ya karanci bangaren kasuwanci amma sai ya yanke shawarar yin kasadar komawa Turai
  • Ya ce ya tsallake tekun Bahar-rum da hamada don komawa turai saboda babu tabbass a Najeriya

Wani matashi da ke zaune a Turai ya bayyana dalilin da yasa ya yanke shawarar barin Najeriya zuwa turai don neman madogara.

A cewar mutumin, ya ga cewa babu wani tabbass a Najeriya don haka ya yanke shawarar komawa Turai.

Matashi dan Najeriya tsaye a gaban mota
"Na tsallaka Teku Da Hamadar Sahara Don Tserewa Daga Kasar, Babu Tabbass a Najeriya" - Matashi Hoto: @italiandavido.
Asali: TikTok

A wani bidiyo da @italiandavido ya wallafa a TikTok, mutumin ya ce ya karanci bangaren kasuwanci a jami'a.

Matashi ya ce babu tabbass a Najeriya, ya koma turai

Sai dai ya koka cewa kasancewar bai san kowa ba a sama da zai taimaka masa, sai ya yanke shawarar tserewa.

Kara karanta wannan

Sauya Naira: Manyan Arewa Sun Fada Wa Shugaba Buhari Abinda Zai Faru Idan Ya Ki Bin Umarnin Kotun Koli

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kuma ce mahaifinsa bai san wani da zai iya yi wa magana ba kasancewar haka tsarin abubuwa suke a Najeriya.

Saboda yadda yake ganin cewa babu wani madogara, sai mutumin ya dauki kasadar tafiya Turai ta hanyar ketare hamadar Sahara da tekun Bahar-rum.

Tuni bidiyon ya yadu kuma ya haifar da martanoni da dama daga yan Najeriya a TikTok.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

@SÀVÀGË DÇ ya ce:

"Wa ya san wani da ya san wani da ya san wani."

@koko ya ce:

"Shekaru 4 a makaranta a Najeriya na kare da kwankwasa kofar mutane don wanke motarsu duk safe. Kwas din watanni 12 a Turai ayyuka na ta nema na."

@Dark Admin ya yi martani:

"Idan har yanzu kana cikin Najeriya ko wani wuri a Afrika ta yamma za ka zata addu'a na aiki idan ka fita waje lokacin ne idanunka za su bude."

Kara karanta wannan

Sabbin Naira: Masani ya fadi kura-kurai 5 da CBN ya yi wajen kawo batun sauyin Naira

@sakartan ya ce:

"A ina tekun Bahur-rum din yake na je na bi? Idan na shafe na shafe kenan."

Matashi ya koka kan yadda mai gidan da yake haya ya kore shi

A wani labari na daban, wani matashi dan Najeriya ya koka kan yadda mai gidan da yake haya ya ba shi takardar tashi daga gidansa bayan ya kashe miliyoyin kudi wajen gyaran gidan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng