Bwacha vs Kefas: Wadanda Ke Tseren Zama Gwamna a PDP da APC a Jihar Taraba

Bwacha vs Kefas: Wadanda Ke Tseren Zama Gwamna a PDP da APC a Jihar Taraba

Jihar Taraba na daya daga cikin jihohin da siyasarsu ke daukar hankali, musamman, yadda ‘yan takarar jihar ke yawan kasancewa kiristoci duk da kuwa adadin musulmai sun fi yawa.

A zaben bana ma bata sauya zabe ba, jam’iyyun siyasa guda biyu mafi shahara a Najeriya; PDP a APC sun tsayar da ‘yan takararsu.

To amma, meye kuka sani game da wadannan ‘yan takarar gwamna a jihar da ke Arewa maso Gabashin Najeriya?

Legit.ng Hausa ta tattaro muku bayanai masu muhimmanci da ya kamata ku sani game da Sanata Emmanuel Bwacha na jam’iyyar APC da Agbu Kefas na jam’iyyar PDP.

Sanata Emmanuel Bwacha na jam’iyyar APC

Tarihin dan takarar gwamnan takara a APC
Sanata Emmanuel Bwacha, dan takarar gwamna a APC na Taraba | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

1. Haihuwarsa

Kara karanta wannan

Jerin 'Yan Takarar Gwamna 3 da Aka Raina Kuma Zasu Iya Ba Da Mamaki a Zaben Gwamnoni

An haifi Bwacha a ranar 15 ga watan Disamban 1962 a karamar hukumar Donga da ke jihar ta Taraba.

2. Karantunsa

Bayan kammala firamare da sakandare, dan siyasan ya yi difloma a fannin aikin gwamnati a jami’ar Calabar, kafin daga bisani ya fara aikin gwamnati gadan-gadan.

3. Aikin gwamnati

A lokacin da yake aikin gwamnati, ya yi kwamishina a lokacin mulkin Jolly Nyame, gwamnan Taraba tsakanin 1999 zuwa 2003.

4. Siyasarsa

Daga baya, Bwacha ya shiga siyasa, inda ya ci nasarar lashe zaben dan majalisar wakilai a tarayya mai wakiltar Donga/Ussa/Takum tsakanin 2003 zuwa 2007.

A wancan lokacin, ya kasance shugaban kwamitin harkokin ‘yan sanda na majalisa. Sai dai, a 2007, ya rasa zaben sanata da ya nema da ma kujerarsa ta dan majalisa.

A 2011, Bwacha na yi nasarar lashe zaben fidda gwanin sanata ba tare da wata doguwar hamayya ba.

A watan Afrilun 2011 aka sanar da ya ci zaben sanata tare da kuri’u 106,172, inda ya lallasa dan takarar ACN na wancan lokacin mai suna Aliyu, wanda ya samu kuri’u 80,256.

Kara karanta wannan

APC Na Tsaka Mai Wuya, Ɗan Takarar Gwamna Ya Janye Daga Takara Kwana 4 Gabanin Zabe

5. Zaben 2023

A halin da ake ciki, Bwacha ne dan takarar gwamnan jam’iyyar APC a jihar Taraba bayan da ya zama cikakken mamban jam’iyyar mai ci a Najeriya.

Agbu Kefas, dan takarar gwamnan PDP

Tarihin dan takarar gwamnan PDP a Taraba
Agbu Kefas, dan takarar gwamnan Taraba a PDP | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

1. Rayuwarsa

An haifi Kefas a ranar 12 ga watan Nuwamban 1970 a Wukari ta jihar Taraba da ke Arewa maso Gabashin Najeriya.

Yana da mata mai suna Patience da kuma yara hudu.

2. Karantunsa

Bayan kammala makarantun firamare da sakandare, yana matashi ya tsunduma makarantar sojoji ta Nigerian Defence Academy, inda ya yi digiri a fannin siyasa da ilimin tsaro a 1994.

Ya kuma yi digiri na biyu a jami’ar Ibadan, inda ya karanta Legal Criminology & Security Psychology a 2005, ya kara wani digirin na biyu a fannin aikin gwamnati a jami’ar Delta a 2008.

Ya kuma samu takardun shaidar karatu daga manyan jami’o’in duniya, ciki har da Harvard da ke Amurka da dai sauransu.

Kara karanta wannan

2023: Gwamnan jihar Arewa ya sha jar miya, 8 cikin 13 na 'yan takarar gwamna sun janye masa

3. Aikin gwamnati

Ahalin Kefas sanannu a jihar da yin hidima a rundunar sojin Najeriya, saboda haka shima ba a barshi a baya ba, kasancewarsa dalibin NDA, ya yi aikin soja.

A cewar rahoto, ya shafe shekaru 21 yana aikin soja kafin daga bisani ya yi ritaya ya kama wata harkar ta daban.

4. Siyasarsa

Bayan ritaya a aikin soja, Kefas ya samu aiki a NIMASA, inda aka ba shi mukami daga cikin manyan daraktocin gudanarwa na hukumar daga 2013 zuwa 2015.

Ya kuma kasance mamban kwamitin shugaban kasa kan shirin kawo dauki na Arewa maso Gabashin Najeriya daga 2016 zuwa 2019.

Daga bisani, ya zama cikakken dan siyasa, inda ya zama shugaban jam’iyyar PDP a jihar ta Taraba a 2020.

5. Zaben 2023

A shekarar 2022, kefas ya bayyana aniyarsa ta zama gwamnan jihar Taraba a karkashin inuwar jam’iyyar PDP mai lema.

Ya yi takara a zaben fidda gwanin jam’iyyar, ya kuma yi nasarar lashe zaben, duk da an kai ruwa rana kan tikitinsa.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Saura kwanaki zabe, an sace dan takarar majalisar dokokin wata jiha

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.