"Ku Kai Rahoton Bankuna Da Suka Ƙi Karɓar Tsofaffin Kuɗi" Soludo Ga Mutanen Anambra
- Gwamnan jihar Anambra, Godwin Emefiele, ya shawarci al'ummar jihar da su cigaba da amfani da tsofaffin kuɗi
- Gwamnan yace ya samu tabbaci daga wajen gwamnan CBN kan cewa al'umma za su iya cigaba da amfani da tsofaffin kuɗin
- Gwamnan ya kuma sanar da hukunci mai tsauri da gwamnatin sa zata ɗauka kan bankunan da suka ƙi karɓar tsofaffin kuɗin a hannun mutane
Anambra- Gwamnan jihar Anambra, Chukwuma Soludo, ya buƙaci al'ummar jihar da su cigaba da aiki da takardun tsofaffin kuɗi sannan su kai rahoton bankuna da suka ƙi karɓar tsofaffin kuɗin. Rahoton Punch
Gwamnan ya bayar da wannan sanarwar ne a ranar Litinin a shafin sa na Facebook inda yake cewa gwamnan CBN, Godwin Emefiele, ya tabbatar masa da cewa bankuna za su iya bayar wa da karɓar tsofaffin kuɗi daga hannun al'umma.
A kalamansa:
“Babban bankin Najeriya (CBN) ya umurci bankuna da su bayar da tsofaffin kuɗi sannan su karɓe su a hannun kwastomomi. Telolin bankuna za su samar da lambobin yin ajiya.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
"Sannan ba a iyakance adadin lokacin da mutane ko kamfanunnika za su iya kai kuɗin su ba."
"Gwamnan CBN ya bayar da wannan umurnin ne a taron kwamitin bankuna wanda aka gudanar a ranar Lahadi, 12 ga watan Maris 2023. Gwamnan, Dr Godwin Emefiele,
"Shine ya tabbatar min da hakan ta wayar tarho a daren ranar Lahadi."
“Saboda haka ana shawartar al'ummar jihar Anambra da su cigaba da harkokin kasuwancin su da takardun tsofaffin kuɗin N200, N500 da N1000 da sababbin takardun kuɗin ba tare da wani shakku ba."
“Haka kuma mutane su kai rahoton duk bankin da ya ƙi karɓar ajiyar tsofaffin kuɗin. Gwamnatin jihar Anambra ba wai kawai zata kai rahoton wannan bankin wajen CBN bane,
"Amma zata kulle reshen bankin da aka samu na aikata hakan nan take."
Gwamnan CBN Ya Shiryawa Tinubu Sababbin Makarkashiya a Zaben Gwamnoni
A wani labarin na daban kuma, ana zargin gwamnan babban bankin Najeriya da shiryawa Bola Tinubu wata sabuwar maƙarƙashiya.
Ana zargin Godwin Emefiele da yin amfani da kujerar sa wajen kawo wa Tinubi cikas a zaɓen gwamnoni dake tafe.
Asali: Legit.ng