Dukiyar Dangote Abdul Samad Ta Karu da Sama da N300bn a Mako Guda, Adenuga Ne Na 3
- Aliko Dangote da Abdul Samad Rabiu sun ga kari a yawan dukiyarsu cikin mako guda, kamar yadda kafar Forbes ta bayyana
- Arzikin Dangote ya karu da $776m, inda aka ce hakan ya samu ne daga zallan ribar da ya ci a sashen hannun jarin siminti na kamfaninsa
- Mike Adenuga, attajiri na uku a Najeriya har yanzu nan kan matsayinsa, ma’ana yana bayan Dangote da Abdul Samad
Aliko da Dangote da Abdul Samad Rabiu, fitattun attajiran Najeriya sun ga kari mai girma a yawan dukiyar da suka mallaka cikin mako guda (Daga ranar Lahadi 4 ga watan Maris zuwa Asabar, 12 ga watan Maris na 2023).
A bangare guda, daya daga cikin attajiran Najeriya, Mike Adunuga ya ci gaba da kasancewa a matsayinsa ba tare da wani kari ba a cikin makon da ya gabata.
A cewar kafar Forbes mai bin kwakwaf din attajiran duniya, dukiyar Dangote ta tashi daga $13.9bn a ranar 4 ga watan Maris zuwa $14.2bn a ranar 12 ga watan na Maris, inda ya samu karin akalla $300m (N138.1bn).
Ana kyautata zaton cewa, karin da Dangote ya samu a dukiyarsa na da nasaba da ciniki da kuma ribar da ya samu a kamfaninsa na siminti.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A cikin makon, an ruwaito cewa, farashin hannun jari daya a kamfanin simintin Dangote ya tashi daga N278 zuwa N288.
Abdulsalam Rabiu
A bangaren Abdul Samad, kudin nasa sun tsaya ne a kan $8.2bn a ranar 12 ga watam Maris, wanda ya nuna ya ci ribar $500m (N230.2bn) idan aka kwatanta da yawan dukiyarsa ta ranar 4 ga watan Maris; $7.7bn.
Karin da Abdul Samad ya samu tana da nasaba ne da karin riba da ya samu a kamfaninsa na BUA Group mai samar da siminti, sukari da fulawa da sauran nau’ikan kayan masarufi.
Mike Adenuga
A bangaren Mike Adenuga, labarin ya sha bamban, domin shi dai dukiyarsa a tsaye take cak a inda take da, inda aka sake samun gibi tsakaninsa da sauran attajiran kasar.
Duk da haka, yana daya daga cikin attajiran Najeriya masu fada a ji, kuma kamfaninsa Globacom ne na biyu a jerin kamfanonin sadarwa a Najeriya da kuma Conoil a matsayin kamfanin man fetur shahararre a Afrika.
A baya kadan, Dangote ya ba da shawarin rufe duk wata harkallar shigowa da tufafi daga kasahen waje.
Asali: Legit.ng