Ban Son A Kashe Ni: Dan Chinan Da Ake Tuhuma Da Kisan Ummita Ya Bayyanawa Kotu

Ban Son A Kashe Ni: Dan Chinan Da Ake Tuhuma Da Kisan Ummita Ya Bayyanawa Kotu

  • Babban kotu a jihar Kano na cigaba da sauraron karar dan kasar Sin da ake zargin ya kashe yar Najeriya
  • Dan Chinan ya bayyanawa kotu cewa bai yi niyyar kashe Ummita ba kuma bai son a kashe shi
  • Alkalin kotu ya dage zaman zuwa karshen wata bayan kammala zaben gwamnoni a Najeriya

Kano - A ranar Alhamis, 10 ga Maris, 2023, an cigaba da sauraron karar da gwamnatin jihar Kano ta shigar kan wani dan kasar Sin, Frank Geng-Quangrong, wanda ake tuhuma da kisan wata yar jihar Kano, Ummukulthum Sani.

Frank ya bayyana cewa bai yi niyyar kashe Ummita ba kuma ta ji masa rauni a marainansa, rahoton TheCable.

Lauya Muhammad Dan’azumi, ya turke Frank Dan China inda yayi masa tambayoyi bisa tuhumar da ake masa.

Ummita
Dan Chinan Da Ake Tuhuma Da Kisan Ummita Hoto
Asali: Twitter

Kara karanta wannan

"Ta Ji Min Rauni A Maraina": Dan Chinan Da Ya Kashe Ummita Ya Bayyanawa Kotu

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Frank Dan China ya bayyanawa kotu cewa:

"Ita ta turo min bidiyon da kanta. Ban yi niyyar kashe Ummukulsun ba kuma ban son a kashe ni."
"Ta ji mini ciwo a maraina kuma ba zan iya nunawa kotu ba. Wannan ya sabawa al'adarmu da China kuma ni Musulmi ne."

Antoni Janar na jihar Kano, Abdullahi-Lawan ya bayyanawa kotu cewa a ranar 16 ga Satumba, 2022, wanda ake tuhuma ya burmawa marigayiya Ummita wuka a gidansu dake Janbulo Quarters, Kano.

Frank dan China kuwa ya musanta wannan tuhuma da ake masa.

Alkali Sanusi Ado-Ma'aji bayan sauraron hujjojin ya dage zaman zuwa ranar 29 ga Maris domin cigaba da zaman.

Dan Chinan Nan Da Suke Soyayya Da Ummita Da AKe Zargi Kuma Ya Kasheta A Gida Yace Ya Kashe Mata Kudi Kusan N60m

Mun kawo muku cewa a shekarar data gabata ne aka samu wani dan kasar Sin da zargin kashe budurwarsa, kan cin amanarsa ko kuma yaudararsa

Kara karanta wannan

"Ba Mu Ji Dadi Ba": Kwankwaso Ya Fusata, Ya Yi Allah Wadai Da Belin Ado Doguwa

Tun a lokacin aka gurfanar dashi a gaban kotu, kuma kotu ta dage shari'ar har sai an samu tafintan da zai ringa fassara masa shari'a zuwa yarensa

A zaman kotun farko da aka fara gudanarwar dan China ya musanta zargin tare da nuna kazafi ake masa.

Haka kuma daga baya ya bayyana irin makudan kudaden da ya kashewa Ummita kimanin milyan sitttin (N60m),

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida