Dan Najeriya Ya Kashe Miliyoyi Wajen Gyara Gida, Mai Gidan Ya Bashi Takardar Tashi

Dan Najeriya Ya Kashe Miliyoyi Wajen Gyara Gida, Mai Gidan Ya Bashi Takardar Tashi

  • Wani matashi dan Najeriya ya fito don ba da labarin abun da ya fuskanta a hannun wani mai gidan haya a Lagas
  • A wani labari da ya wallafa a Twitter, mutumin ya ce ya karbi hayar gida a birnin sannan ya kashe miliyoyi wajen gyara shi
  • Sai dai ya kadu da ganin cewa bayan watanni shida da komawa gidan, mai gidan ya aika masa takardar tashi

Lagos - Wani matashi dan Najeriya ya bayyana yadda mai gidan da yake haya ya kore shi daga muhallinsa bayan watanni shida.

Mutumin mai suna @folastag a Twitter ya ce abun da ya fi masa ciwo shine cewa ya yi amfani da kudinsa wajen gyara gidan.

Hoton gida da wani matashi
Dan Najeriya Ya Kashe Miliyoyi Wajen Gyara Gida, Mai Gidan Ya Bashi Takardar Tashi Hoto: Twitter/@folastag da Yana Iskayeva/ Getty Images.
Asali: UGC

A cewarsa, ya koma cikin gidan bayan ya kashe miliyoyi wajen mayar da shi yadda yake son ya kasance.

Kara karanta wannan

An Gano Wanda Ya Haddasa Jirgin Kasa Ya Murkushe Motar Ma'aikatan Gwamnati a Legas

Mai gidan haya a Lagas ya kori wani mutum bayan watanni 6

Ya sha mamaki lokacin da mai gidan hayan ya sammace shi da takardar tashi ba tare da wani kwakkwaran dalili ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Mai gidan ya yi ikirarin cewa yana so ya mayar da iyalinsa gidan, don haka yake so a kwashe komai daga ciki.

Ya rubuta a Twitter

"Na fuskanci yanayi mafi muni a rayuwata tsakanin Agustan 2022 da Janairun 2023. Bayan na koma sabon gidan da na karba a Fabrairun 2022, na kashe miliyoyi don gyara da kawata gidan. Mai gidan hayan ya aiko mun da takardar tashi bayan watanni 6."

Wani abun mamaki shine cewa mai gidan ya sake sanya gidan a haya ne bayan ya fatattaki wanda ke ciki a da.

Ya ce mai gidan dan sa ido ne wanda ke yawan yawo a harabar gidan tsirara.

Kara karanta wannan

Dumu-dumu kenan: Bidiyo mai daukar hankali na yadda barci ya kwashe yaro na tsaka da barnata Milo

"Dan sa ido ne, wanda ke shigowa akai-akai don leka masu haya. Yana yawan yawo zindir a gidan(hatta da rana)."

Kalli wallafar a kasa:

Jama'a sun yi martani

@OgbeniDipo ya ce:

"Ina mai baka hakuri game da halin da ka shiga. Wannan abun bakin ciki ne."

@TomiwaImmanuel ta yi martani:

"Wannan abun na faruwa a fadin Lagas, kuma yana da ban tsoro. Ina mai baka hakuri da fuskantar wannan da ka yi, Fola. Ina fatan ka samu matsuguni yanzu?"

Budurwa ta yi karo da iyayenta a 'go slow'

A wani labari na daban, wata budurwa ta yi kicibis da iyayenta a 'go slow' yayin da take sauri don ganin ta isa gida ba tare da an ankara cewa ta yi dare a waje ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng