Yan Kasuwa a Enugu Sun Zo Da Nasu Tsarin Game da Karban Tsohon N500 da N1000

Yan Kasuwa a Enugu Sun Zo Da Nasu Tsarin Game da Karban Tsohon N500 da N1000

  • Har yanzun abubuwa ba su daidaitu ba a mafi yawan sassan ƙasar nan game da amfani da tsoffin N500 da N1000
  • A jihar Enugu, yan kasuwa da mazauna sun ce sam ba zasu amsa ba domin har yau mahukunta ba su ce komai ba
  • Kotun Koli ta yanke hukuncin tsawaita wa'adin amfani da tsohon N200, N500 da N1000 har zuwa watan Disamba

Enugu - Wasu 'yan kasuwa a jihar Enugu sun kafe kan bakatsu cewa ba zasu karbi tsoffin N500 da N1000 ba duk da hukuncin Kotun koli da ya tsawaita wa'adin amfani da su.

Da yawan 'yan kasuwan da suka zanta da hukumar dillancin labarai (NAN) a jihar ranar Alhamis, sun ce har yanzu ba su ji daga bakin mahukunta masu alhaki kan lamarin ba.

Takardun tsoffin naira.
Yan Kasuwa a Enugu Sun Zo Da Nasu Tsarin Game da Karban Tsohon N500 da N1000 Hoto: thenation
Asali: UGC

A cewarsu, ko mutum ya karba zai wahala ya iya kashe su domin mafi akasarin mutane ba su yarda ka basu tsoffin takardun kuɗin, kamar yadda The Nation ta rahoto.

Kara karanta wannan

Naira: Gwamnan APC Ya Fusata, Ya Faɗi Babban Laifin Duk Wanda Ya Ƙi Karban Tsoffin N500 da N1000

Wani mai Keke Nafef, Mista Uche Ossai, ya ce har yanzu bai fara karban tsohon naira ba saboda zai wahala ya iya amfani da su domin gidajen mai ba su karba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Haka nan wata mai sana'ar sayar da kayan abinci, wacce ta nemi a sakaya sunanta ta ce ba zata karbi tsohon kuɗi ba saboda duk wanda ta ba ba zai amsa ba

"Masu sufuri sun ki yarda ku karbi tsohon N500 da N1000, don haka kar ku yi tsammanin zan amsa daga hannun wasu saboda daga karshe ni ce zan yi asara," inji ta.

Mista Jude Okoye, Mai shagon sayar da kayan amfanin yau da kullum a kasuwar Mayor, ya shaida wa NAN cewa ya fi aminta kwastomomi su tura masa kuɗi ta banki da su haɗa shi da tsohon kuɗi.

Kara karanta wannan

Rudani: DSS ta Gargadi 'Yan Najeriya, Ta Ce Akwai Munanan Abubuwan Da Za Su Faru Bayan Zaben Gwamnoni

Haka zalika wata mai shagon kwalliya da gyaran jiki, Misis Jacinta Nweke, ta ce ma'aikatan Asibitin koyarwa na jami'ar Najeriya (UNTH) basu karbi tsohon kuɗi ba lokacin da zata biya bil ɗin Asibiti.

"Lokacin da na je biyan kudi a UNTH bayan Likita ya duba ni, ba su karbi tsohon kuɗin da na ba su ba, suka ce mun ba su samu umarni daga mahukunta ba," inji ta.

Wata mata mai zama a Anguwar Achara layout, Miss Gloria Okoroafor, ta ce mai Nafef din da ya kawo ta gida ma bai karbi tsohon kuɗin da ta ba shi ba.

Ta ƙara da cewa Direban Nafef din ya gaya mata cewa CBN kaɗai ke karban tsohon kuɗin kuma har yanzu bai ji babban bankin ya umarci mutane su karba ba.

Daina Karban Tsohon N500 da N1000 Saba Wa Doka Ne, Gwamnan Ondo

A wani labarin kuma gwamnan jihar Ondo ya roki mutanen jiharsa su taimaka su ci gaba da karban tsoffin N500 da N1000.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Gobara ta kama a kasuwar wata jiha, ta yi kaca-kaca da kayayyakin miliyoyi

Gwamna Oluwarotimi Akeredolu, ya bayyana mummunar illar da rashin karban kuɗin zai haifar ga talakawa kuma sabawa doka ne.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262