Yanzu Yanzu: Kotu Ta Garkame Tsohon Mataimakin Gwamnan Imo a Gidan Gyara Hali

Yanzu Yanzu: Kotu Ta Garkame Tsohon Mataimakin Gwamnan Imo a Gidan Gyara Hali

  • Kotun majistare ta Owerri ta garkame tsohon mataimakin gwamnan jihar Imo, Gerald Irona, a gidan gyara hali
  • Mai shari'a C. N Ezerioha ta ba da umurnin tsare mata Irona a gidan maza a yau Alhamis, 9 ga watan Maris
  • Kotun ta kuma ce basu da hurumin sauraron shari'ar Irona bayan ta saurari bangaren mai kara da wanda ake kara

Imo - A ranar Alhamis, 9 ga watan Maris, wata kotun majistare da ke Owerri, ta garkame tsohon mataimakin gwamnan jihar Imo, Gerald Irona, a gidan gyara hali.

Mai shari'a a kotun, C. N Ezerioha, ta ba da izinin tsare Irona a gidan gyara hali na Owerri bayan ta saurari jawabai daga bangaren lauyan mai kara da lauyan wanda ake kara, rahoton Punch.

Tsohon mataimakin gwamnan jihar Imo da wasu mutane a bayansa
Yanzu Yanzu: Kotu Ta Garkame Tsohon Mataimakin Gwamnan Imo a Gidan Gyara Hali
Asali: Facebook

Ta kuma bayyana cewa kotun ba ta da hurumin sauraron shari'ar.

Kara karanta wannan

Saura kiris zaben gwamna: Sojoji sun kama katin zabe 1,671 da takardun aikin zabe a wata jiha

Yadda yan sanda suka kama tsohon mataimakin gwamnan Imo

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa jami’an tsaro sun kama tsohon gwamnan a ranar Laraba, 8 ga watan Maris, a gidansa da ke Owerri, kamar yadda wasu da abun ya faru a idonsu suka bayyana.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Shaidun da suka nemi a sakaya sunansu sun ce:

“Wasu jami’an tsaro daga rundunar yan sandan jihar Imo sun kama tsohon mataimakin gwamnan jihar Imo, daga gidansa da ke Owerri. Sun zo gidansa ne cikin bakin kaya. Suka tafi da shi ofishin yan sandan jihar sannan suka ce sun kama shi ne bisa umurnin da aka bayar daga sama. Yanzu an tsare shi a ofishin yan sandan jihar.
"Sun yi zargin cewa laifinsa shine saboda ya yi wata sanarwa cewa za a mayar da jihar Imo ta zama babu shugabanci yayin fafatawar Gwamna Hope Uzodimma da tsohon Gwamna Emeka Ihedioha a kotun koli idan har aka cire Ihedioha daga mulki.

Kara karanta wannan

Mazan Fama: Sojoji Sun Kai Samame Sansanin 'Yan Bindiga, Sun Ceto Kwamishina

"Kuma cewa yan sanda sun ayyana neman Irona ruwa a jallo a baya saboda mallakar kayayyakin gwamnati ba bisa ka'ida ba da sai sauran laifuka."

Wasu majiyoyi kuma sun yi zargin cewa an kama Irona ne bisa umurnin da gwamnatin jihar ta samu daga kotu.

A wani labari na daban, mun ji cewa an yi kazamin karo tsakanin yan daban siyasa na jam'iyyun PDP da APC a jihar Bauchi lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutum daya da jikkata wasu 15

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Tags: