Daina Karban Tsohon N500 da N1000 Saba Wa Doka Ne, Gwamnan Ondo

Daina Karban Tsohon N500 da N1000 Saba Wa Doka Ne, Gwamnan Ondo

  • Gwamna Akeredolu na jihar Ondo ya koka kan yadda mutane suka ƙi karban tsohon takardun naira
  • Ya ce kin karban kuɗin bayan hukuncin Kotun koli tamkar karan tsaye ne ga tanadin doka a Najeriya
  • Ya kuma roki mazauna jihar Ondo su taimaka su ci gaba da hada-hada da tsoffin N500 da N1000 don rage radadi

Ondo - Gwamnan jihar Ondo, Oluwarotimi Akeredolu, ya bayyana matakin 'yan kasuwa da wasu mutane na ƙin karban tsoffin kuɗi da saɓa wa tanadin doka a Najeriya.

Gwamnan ya yi wannan furucin ne a wani jawabin kai tsaye da aka watsa a jiharsa da ke kudu maso yammacin Najeriya, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Gwamnan Ondo, Oluwarotimi Akeredolu
Gwamna Oluwarotimi Akeredolu Na jihar Ondo Hoto: Oluwarotimi Akeredolu
Asali: UGC

Haka nan gwamna Akeredolu na jam'iyyar APC ya koka kan yadda mafi yawan yan kasuwa da masu saye da sayarwa suka nuna ba zasu karbi tsohon kuɗin ba.

Kara karanta wannan

Sabuwar Matsala Ta Bullo Yayin da Bankuna Suka Fara Zuba Tsoffin N500 da N1000 a ATM

Ya ce rashin amsar tsoffin takardin nairan zai ƙara durkusad da tattalin arzikin ƙasa kuma zai yi mummunar illa ga hada-hadar cikin gida da harkokin sufuri.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Idan baku manta ba Kotun koli ta yanke hukuncin tsawaita wa'adin amfani da tsoffin kuɗin har zuwa 31 ga watan Disamba, 2023.

Gwamnan ya ce:

"Saboda haka abun damuwa ne a gare ni ganin mafi yawan mutane musamman 'yan kasuwa, Direbobi, masu aski, Kanikawa sun ƙi karban tsohon kuɗin wanda hakan ya kara jefa mazauna cikin wahalar rayuwa."
"Ina faɗa maku cewa rashin karban tsohon N1000 da N500 da muke yi mu abun zai shafa, zai gurgunta kasuwancin mu, ya naƙasa tattalin arziƙinmu kuma ya mana illa mai girma."

Bugu da ƙari, Akeredolu ya yi kira ga bankuna su saki sabbi da tsoffin takardun naira a dukkan wuraren cire kuɗi domin rage cunkoson jama'a a harabar bankuna.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Dumi: CBN Ya Amince a Ci Gaba da Amfani da Tsoffin Naira, Sabbin Bayanai Sun Fito

Dan Allah ku riƙa karban tsohon naira - Gwamna

The Nation ta tattaro gwamnan na cewa:

"Ina amfani da wannan dama na roke ku baki ɗaya mazauna jihar Ondo masu albarka, dan Allah ku ci gaba da karban tsoffin kuɗi tare da sabbin kamar yadda doka ta tanada."
"Ka da ku ƙara jefa kanmu cikin tashin hankali da ƙuncin rayuwa, Dan Allah mu karba, mu kashe kuma mu yi hada-hada da tsohon takardun naira ba tare da wani shamaki ba."

A wani labarin kuma kun ji cewa Bankuna Sun Ci Gaba da Baiwa Mutane Takardun N500 da N1000

Sai dai duk da bankuna na ba da tsohon kuɗin, wasu yan kasuwa sun ce ba zasu karba ba har sai shugaban kasa, Muhammad Buhari, ya yi jawabi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262