Hukumar INEC Ta Tabbatar Da Emmanuel Bwacha Matsayin Dan Takaran Gwamnan Taraba na APC
- Hukumar INEC ta bayyanawa kotu cewa ta daura sunan Emmanuel Bwacha a shafinta na intanet
- Ta tabbatar da Sanatan a matsayin sahihin dan takaran kujerar gwamnan jihar Taraba na APC
- An kai ruwa rana tsakanin jigogin jam'iyyar APC kan dan takarar gaskiya da zai wakilci jam'iyyar
Jalingo - Babban kotun tarayya dake Jalingo jihar Taraba, da hukumar zabe ta kasa (INEC) a ranar Laraba ta bayyana cewa Sanata Emmanuel Bwacha ne sahihin dan takarar gwamnan jihar Taraba karkashin jam'iyyar All Progressives Congress(APC).
INEC ta tabbatar da cewa sunan Emmanuel Bwacha ne a shafinta na yanar gizo kuma tayi kira ga jama'a suyi watsi da labaran boge cewa babu sunansa, rahoton Tribune.
Alkali Bala KS Usman a hukuncin da ya yanke kan karar da APC ta shigar da INEC na kin sanya sunan Bwacha a yanar gizo matsayin dan takaran APC a Taraba, yace hukumar ba tada hakkin cire sunan Bwacha tunda an yi sabon zaben fidda gwani.
INEC kuwa a jawabinta ta bayyana cewa sam bata cire sunan Bwacha daga shafinta na yanar gizo ba.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Tace ana kammala sabon zaben fidda gwani suka mayar da sunansa a matsayin sahihin dan takaran gwamnan jihar.
Kakakin kwamitin kamfen Bwacha, Mr Aaron Artimas, ya ce wannan hukunci da kotu tayi nasara ce ga Taraba.
Ya ce hukuncin ya kawo karshen labaran kanzon kuregen da PDP ke yadawa cewa duk wanda ya zabi APC yayi asarar kuri'arsa saboda ba tada dan takara.
A cewarsa:
"Kotu da INEC sun wanke karerayin PDP a kan APC kuma yanzu yan Taraba zasu iya zaben Sanata Emmanuel Bwacha mastayin gwamnan jihar Taraba. Sunan Bwacha na shafin yanar gizon INEC."
"Ina kira ga al'ummar jihar Taraba su sani cewa Bwacha ne dan takarar gwamnan APC na Taraba."
Kotu ta yi hukuncin karshe kan wada zai rike tutar PDP a zaben gwamnan Taraba
A wani labarin kuwa, kotun koli ta tabbatar da tsohon soja Kefas Agbu matsayin sahihin dan takarar gwamnan jihar Taraba a karkashin inuwar jam'iyyar PDP, Channels Tv ta ruwaito.
Wannan hukuncin ya tabbatar da hukuncin kotun daukaka kara na Yola a jihar Adamawa da ya yi watsi da batun kalubalantar sahihancin takarar Kefas.
An samu rikici a jam'iyyar PDP ta jihar Taraba ne bayan kammala zaben fidda gwamin da ya samar da Kefas a shekarar da ta gabata.
Asali: Legit.ng