DSS Ta Kama Yan Jam'iyyar PDP 3 A Kaduna 'Kan Shirin Tada Rikici' Yayin Zaben Gwamna Da Majalisun Jiha
- Sa'idu Adamu, mataimakin direkta na kwamitin kamfen din takarar gwamna na jam'iyyar PDP a Kaduna ya ce DSS ta kama mambobinsu uku
- Adamu ya bayyana cewa hukumar ta DSS tana zargin mambobin da shirya tada tarzoma yayin zaben gwamna da yan majalisun jiha da ke tafe
- Jigon na PDP ya yi ikirarin cewa gwamnatin jihar Kaduna ta jam'iyyar APC ne ke amfani da hukumomin tsaro don tsorata jam'iyyun hamayya
Jihar Kaduna - Jami'an DSS sun kama Saidu Adamu, mataimakin direkta na kwamitin kamfen din takarar gwamna na jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, a Kaduna.
Jaridar The Cable ta tattaro cewa an kama Adamu a ranar Laraba tare da El-Abbas Muhammed da Talib Muhammed, shugabannin matasa.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Majiyoyi da suke da masaniya kan labarin sun bayyana cewa yan sandan farin kayan sun zargi yan siyasan ne da shirin tada rikici yayin zaben ranar 11 ga watan Maris da ke tafe.
Kakakin PDP ya tabbatar da kama su
Da ya ke tabbatar da kamen a ranar Laraba a hirar wayar tarho, Abraham Alberah, kakakin PDP a Kaduna, ya ce DSS ta kama mutane ukun kan zargin shirin tada zauna tsaye.
Alberah ya kuma yi ikirarin cewa DSS din na shirin kama wasu mambobin kwamitin kamfen din PDP bisa umurnin gwamnatin jam'iyyar APC a jihar.
A cewar Alberah:
"APC na amfani da hukumomin tsaro don tsorata yan jam'iyyun hamayya gabanin kayen da za su sha a zaben gwamna.
"DSS ta musu barazana, tana ikirarin sune ke tada rikici. Babu shakka jam'iyya mai mulki na amfani da hukumomin tsaro don tsorata mu.
"Wadanda DSS ke shirin kamawa sun hada da Victor Bobai, mataimakin direkta, kafar watsa labarai; Reuben Buhari, mataimakin direkta na watsa labarai; Yakubu Lere, mataimakin direkta na harkokin al'umma; Saidu Adamu, mataimakin direkta na kafar watsa labarai da ni kai na, sakataren kwamitin watsa labarai na kwamitin kamfen."
“Ku Sarara Mun, Ku Ma Kun Fadi Zaben Sanata”: Atiku Ya Yi Wa Gwamnonin G5 Da Wike Ke Jagoranta Wanki Babban Bargo
Shugaban Bala Lau Shugaban Izala ya Gargadi Yan Siyasa Kan Maganganun Da Ka Iya Tada Tarzoma
Sheikh Bala Lau, shugaban kungiyar Izala ya gargadi yan siyasa a Najeriya kan yin maganganu da ka iya tada zaune tsaye ga aikin hukumar zabe mai zaman kanta, INEC.
Ya bayyana hakan ne cikin wani sanarwar manema labarai da ya fitar a ranar Talata, 28, ga watan Fabrairu a madadin kungiyar ta Izala.
Asali: Legit.ng