An Kama Mutum 793 da Ake Zargi da Harkallar Miyagun Kwayoyi a Abuja, an Kwato Kwayoyi
- Hukumar NDLEA ta yi nasarar kame masu harkallar kwayoyi da sha a yankuna daban-daban na babban birnin tarayya Abuja
- Hukumar ta kuma bayyana nasarar da ta samu na daura ‘yan kwaya a kan turbar waraka a cikin shekarar da ta gabata
- Ya zuwa yanzu, an shiga 2023, NDLEA na tsammanin samun raguwar sarafa da shan miyagun kwayoyi a kasar nan, inji rahoto
FCT, Abuja - Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) ta kama kilo-giram 13,125 na miyagun kwayoyi tare da kama mutum 798 a cikin shekarar 2022.
Kwamandan NDLEA a Abuja, Mr. Kabir Tsakuwa ne ya bayyana hakan a ranar Talata yayin da yake magana a taron manema labarai kan illolin miyagun kwayoyi a birnin, Daily Trust ta ruwaito.
Tsakuwa ya bayyana cewa, hukumar ta yi nasara a 2022, inda ya kara da cewa, an kama mutane da kayayyakin bugarwa masu yawa.
Ya kuma shaida cewa, shirin farfado da masu shan kwayoyi na haifar da da mai ido a babban birnin tarayya Abuja.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Adadin mutanen da aka kama a Abuja
A cewarsa, an kama jumillar mutane 793 da suka hada da maza 768 da mata 29 a birnin, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Shugaban na NDLEA ya kuma bayyana cewa, an gurfanar da mutum 167 da suka kada da maza 161 da mata shida.
Tsakuwa ya kuma bayyana cewa, an yi nasarar daura mutum 78 da suka hada da maza 74 da mata hudu a kan turba.
Ya kara da cewa, wannan nasara da hukumar ta samu zai rage yawaitar shan miyagun kwayoyi da safararsu a shekarar 2023 da muke ciki.
Hukumar NDLEA ta sha kame masu safarar miyagun kwayoyi da sha a yankuna daban-davan na Najeriya, musamman a shekarar da ta gabata.
Wani Soja Mai Safarar Miyagun Ƙwayoyi Ya Shiga Hannun Hukuma
A wani labarin, kun ji yadda hukumar ta kama wani soja da akr zargi da safarar miyagun kwayoyi duk kuwa da yana aikin tsaro a Najeriya.
An gurfanar da sojan mai shekaru 49, Olanrewaju Lawal, bisa zargin ya shigo da kwayoyin Tramadol da dai sauran haramtattun kayan buguwa.
A lokacin, bayan sauraran batutuwa alkalin kotun ya umarci a ci gaba da ajiye Lawal a magarkama kafin a ci gaba da sauraran kara.
Asali: Legit.ng