An Tsinci Wani Mutum Da Aka Yi Wa Fashin N97,000 A Sume A Gefen Titi Da Kebur A wuyansa A Jigawa

An Tsinci Wani Mutum Da Aka Yi Wa Fashin N97,000 A Sume A Gefen Titi Da Kebur A wuyansa A Jigawa

  • An tsinci wani bawan Allah a sume a gefen titi da kebur a wuyansa a karamar hukumar Kiyawa, Jihar Jigawa
  • Bayan ya farfado a asibitin, mutum ya bayyana cewa a Takur Adua Quaters ya shiga tasi don zuwa kasuwa siyayayya da N97,000 a tare da shi
  • Hukumar NSCDC ta jihar Jigawa ta tabbatar da afkuwar lamarin, ta kuma ce tana aiki tare da sauran hukumomin tsaro don gano wadanda ake zargi

Jihar Jigawa - Hukumar tsaro ta Civil Defense, NSCDC, a ranar Litinin ta gano wani mutum a sume a karamar hukumar Kiyawa, Daily Trust ta rahoto.

Mai magana da yawun hukumar NSCDC na Jigawa, CSC Adamu Shehu ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar.

Bawan Allah
Mutumin da wasu suka shake a tasi suka masa fashin N97,000 a Jigawa. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

Kwana 4 Gabanin Zabe, Kotun Ƙoli Ta Ayyana Halastaccen Ɗan Takarar Gwamnan APC a Jiha 1

Ya ce:

"Yau Litinin 6 ga watan Maris na 2023 misalin karfe 6 na yamma hukumar ta samu kiran neman dauki daga wani Malam Wadari, dagacin Mabara, wani kauye a garin Andaza, karamar hukumar Kiyawa.
"Yana cewa ya samu rahoton an tsinci wani mutum a sume a gefen titi da kebur a wutansa wanda daga bisani aka gano sunansa Umar Ibrahim, dan shekara 58 kuma mazaunin kauyen Sarari, Sakwaya, karamar hukumar Dutse, Jigawa. Yana hanyar zuwa kasuwan Shuwarin ne don siyayya."

Ya ce da isarsu wurin da abin ya faru, tawagar ma'aikatan lafiya na NSCDC sun gano akwai kebur a wuyan wanda abin ya faru da shi da aka yi amfani da shi don shake shi kuma jini na fita daga bakinsa.

An garzaya da shi babban asibitin Dutse don masa magani.

Bayan ya farfado, mutumin da aka sace ya ce ya shiga tasi ne daga Takur Addua Quaters a birnin Dutse tare da wasu fasinjoji uku.

Kara karanta wannan

IWD2023: Mata 2 da Suka Shiga Jerin ‘Yan siyasa 109 da Za su Zama Sanatocin Najeriya a 2023

Ya kara da cewa yana dauke da tsabar kudi N97,000 wanda ya ke son amfani da shi don siyayya a kasuwa.

Bai san abin da ya faru da shi ba sai da ya tsinci kansa a gadon asibiti.

Kwamandan NSCDC ya ankarar da al'umma su dena shiga mota a wajen tasha

A gefe guda, kwamandan jihar, Musa Alhaji Malah, ya yi kira ga al'umma su dena shiga tasi a wajen tasha don kare kansu daga irin hakan.

Ya kuma yi alkawarin aiki tare da sauran hukumomin tsaro don gano wadanda suka aikata laifin.

A wani rahoton kun ji cewa yan sandan jihar Ondo ta kama wata matashiya yar shekara 16 kan zargin halaka wata yar shekara 52, Medinat Aliu, sakamakon bangaje ta yayin rikici kan rijiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164