Yan Sanda Sun Ayyana Neman Dan Takarar Gwamnan APGA Kan Kisan Basarake

Yan Sanda Sun Ayyana Neman Dan Takarar Gwamnan APGA Kan Kisan Basarake

  • Hukumar 'yan sanda a jihar Ebonyi ta ce tana neman dan takarar gwamnan APGA da wasu mutane 9 ruwa a jallo
  • 'Yan sanda na neman damƙe mutane 10 ne bisa zargin hannu a kisan wani Basarake a jihar makon da ya gabata
  • A ranar Litinin kwana 7 kenan aka kashe Basaraken, jam'iyyar APC ta ɗora ayar zargi kan ɗan siyasan

Ebonyi - Rundunar 'yan sandan jihar Ebonyi ta ayyana neman ɗan takarar gwamna a inuwar jam'iyyar All Progressive Grand Alliance (APGA), Ifeanyi Odoh, ruwa a jallo.

Premium Times ta tattaro cewa 'yan sanda na neman Mista Odoh da wasu mutane 9 ne bisa zargin hannu a kisan wani Basarake, Igbokwe Ewa.

Yan sandan Najeriya
Yan Sanda Sun Ayyana Neman Dan Takarar Gwamnan APGA Kan Kisan Basarake Hoto: premiumtimes
Asali: UGC

Yadda lamarin ya faru

Rahoto ya nuna cewa a ranar Litinin makon da ya gaba ne wasu yan bindiga suka yi ajalin Basaraken. Kafin rasuwarsa ya kasance Sarkin a kauyen Umu-Ezekoha, karamar hukumar Ezza ta arewa.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Kutsa Har Ciki Fada, Sun Yi Garkuwa da Matan Sarki 2 da Ɗansa a Jihar Arewa

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Bayan faruwar haka ne, jam'iyyar APC mai mulki ta ɗiga ayar zargi kan ɗan takarar gwamnan APGA da magoya bayansa, ta ce suna da hannu a kisan Basaraken.

Amma Mista Odoh ya musanta zargin da cewa Basaraken da ake magana a kai, wanda suka fito karamar hukuma ɗaya da shi, tamkar mahaifi ya ɗauke shi.

Yan sanda suna neman mutum 10 ruwa a jallo

A yau Litinin, jami'in hulɗa da jama'a na hukumar 'yan sanda, Onome Onovwakpoyeya, a wata sanarwa ya ayyana neman mutane 10 ruwa a jallo kan zargin hannu a kisan.

Jerin sunayen mutanen da ake zargi

Bayan Mista Odah, sauran 9 sun haɗa da, Samuel Onyekachi Aligwe, Peter Orogwu (one boy), Chukwudi Aliewa (Ezza) da kuma Chika Ezealigbo.

Sauran su ne, Nnaemeka Egede, Nnabuike Okohu, Ogobuchi Agbom (ana ce masa Okiri), Nonso Obasi, da kuma Ikechukwu Nwoba wanda ake kiransa da Solid.

Kara karanta wannan

Abin Ban Takaici Cocin Gidan Gwamnati Ta Aso Rock Za'a Rufe ta Na Tsawon Shekara 4 - Okowa

Rundunar 'yan sandan ta kuma roki ɗaukacin al'umma da su taimaka da bayanai sahihai da ka iya kai ga kama waɗan da ake zargin, kamar yadda Vangaurd ta rahoto.

A wani labarin kuma Yan Bindiga Sun Sake Shiga Kaduna, Sun Yi Awon Gaba da Sama da Mutum 10

Wasu mahara sun kai hari wani ƙauye a yankin ƙaramar hukumar Kagarko dake jihar Kaduna, sun yi awon gaba da mutane 12.

Mazauna garin sun ce maharan sun sace wata mata da yayanta guda biyu amma sauran mutane 9 sun gudo daga hannunsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262