Bankuna Sun Garkame Kofofi Yayin da Mutane Suka Kewaye Su Neman Kash

Bankuna Sun Garkame Kofofi Yayin da Mutane Suka Kewaye Su Neman Kash

  • Bankuna sun rufe manyan kofofinsu yayin da mutane suka cika maƙil domin cire kudi daga asusu
  • Wasu ma'aikata sun bayyana cewa sun yi haka ne domin babu tsabar kudi kuma suna dakon umarni daga CBN
  • Wannan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan Kotun koli ta tsawaita wa'adin amfani da tsoffin naira

Lagos - Bankuna da dama sun sa kwaɗo sun datse kofofin shiga yayin da kwastomomi suka mamaye haraba domin cire kuɗi a asusu a jihar Legas.

Daily Trust ta ce Bankunan sun yanke shawarin datse shiga ofisoshinsu ne yayin da suke dakon umarni daga CBN biyo bayan hukuncim da Kotun koli ta yanke.

Harabar reshen Bankin UBA.
Yadda mutane suka yi dafifi a bankin UBA Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Bayanai sun nuna cewa da yawan mutanen da suka durfafi bankuna domin hada-hadar kuɗi ba su ji daɗi ba ganin yadda kiri-kiri aka hana su shiga.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Wahala Ta Ƙare, Wasu Bankuna Sun Fara Baiwa Mutane Tsoffin N500 da N1000

Wani wakilin bankunan ya shaida wa jaridar cewa sun Datse kofofin shiga ne suna jiran umarnin CBN da kuma samar da tsabar kuɗin da zasu baiwa jama'a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Muna dakom umarni ne daga sama game da matsayar da suka ɗauka bayan hukuncin Kotun koli. Muna kuma bukatar takardun kuɗi, tsoffi ko sabɓi domin biyan bukatun kwastomomin mu."
"Babban matsalar da muke fama da ita a 'yan makonnin nan shi ne da yawan mutane suna cire kuɗi ne ba tare da sun kawo ajiya ba, saboda haka muna bukatar Kash daga CBN don cika bukatun mutane."

- A cewar ma'aikacin, wanda ya nemi a sakaya sunansa.

Haka nan wani babban ma'aikaci ya tabbatar da cewa ma'aikata sun fito aiki amma sun hana mutane shiga harabar domin kauce wa tashin-tashina da rashin bin doka.

"Nan ba da jimawa ba CBN zai aiko mana da matsaya, ba zamu yi gaban kan mu ba sai mun ji daga sama. Kar ku manta bankuna ba su cikin waɗanda aka shigar ƙara."

Kara karanta wannan

Gaba da Gabanta: 'Yan Bindiga Sun Gamu da Mutuwa Yayin da Suka Yi Yunkurin Sace Matashi a Bauchi

An hangi mutane da yawa sun jera dogon layuka a bakin Get ɗin wasu bankuna a kewayen Ikeja, Alausa, Surulere da sauransu.

Bankuna Sun Ci Gaba da Baiwa Mutane Takardun N500 da N1000

A wani labarin kuma kun ji cewa Wasu Bankuna sun fara biyan kwastomomi da tsoffin takardun naira a Kano da Abuja

Binciken da aka gudanar yau Litinin ya nuna wasu bankuna a Abuja da Kano sun fara biyan 'yan Najeriya kuɗi da tsohon N500 da N1000. Har yanzun dai CBN bai ce uffan ba bayan Kotun koli ta yanke hukuncin tsawaita wa'adin amfani da tsoffin kuɗin zuwa karshen watan Disamba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262