Bayan Kwanaki a Garkame, Kotu Ya Ba da Belin Hon. Ado Doguwa

Bayan Kwanaki a Garkame, Kotu Ya Ba da Belin Hon. Ado Doguwa

  • Kotun majistaren jihar Kano ya ba da belin Ado Doguwa da ake zargi da hannu a kashe-kashe da tashin hankali a jihar
  • An ce akwai hannun Ado Doguwa a mutuwar wasu mutane a ranar zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayya a Kano
  • An ba dan majalisar sharuddan da zai bi nan da zuwa wani lokaci har bayan zaben gwamnoni da za a yi a kasar

Jihar Kano - Yanzu muke samun labarin cewa, kotu ya ba da belin Hon. Ado Doguwa, wani jigon siyasar APC kuma dan majalisar tarayya daga jihar Kano, Freedom Radio ta ruwaito.

A baya an tsare Doguwa ne bisa zarginsa da hannu a mutuwar wasu mutane a lokacin zaben shugaban kasa da na 'yan majalisu a Kano.

An tsare Doguwa na tsawon kwanaki biyar bayan da 'yan sanda suka gurfanar dashi a gaban kotun majistare da ke Kano.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Wahala Ta Ƙare, Wasu Bankuna Sun Fara Baiwa Mutane Tsoffin N500 da N1000

Kano: Yadda aka ba da belin Ado Doguwa
Jihar Kano, jihar da Ado Doguwa yake wakilta a Majalisar Tarayya | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Sai dai, lauyan Doguwa, Nureini Jimoh (SAN), ya nemi belin wanda yake karewa daga alkalin kotun, Muhammad Nasir Yunusa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya bayyana cewa, tsare Doguwa ya yi kama da take hakkinsa na dan adam, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

A cewar Jimoh, tun da an ce ana zargin Doguwa da hannu a kisan kai da kuma mallakar makamai ba bisa ka’ida ba, kotun majistare bai da hurumin yin shari’ar.

Sharadin belin Doguwa

Bayan sauraran batutuwa, mai shari’a Yunusa ya ba da belin Doguwa tare da ba shi sharadin kawo mutum biyu masu tsaya masa.

Hakazalika, ya ce daya daga cikin masu tsayawa dan majalisar dole ya kasance basaraken gargadiya daya kuma ya kasance sakataren dindindin a ma’aikatar gwamnatin tarayya ko ta jiha.

Har ila yau, ya umarci Doguwa da ya kawo takardunsa na ketare kasa, wanda kotun zai ba shi duk lokacin da ya bukaci barin kasa.

Kara karanta wannan

An Kuma: 'Yan Bindiga Sun Sake Kai Sabon Mummunan Hari a Jihar Kaduna

Kuma an ce, dole ya dawo da takardun bayan dawowa daga duk wata tafiya da ya yi a wajen kasar.

Daga karshe, kotun ya bukaci Doguwa da ya nesanta kansa da mazabarsa a lokacin zaben gwamna da na ‘yan majalisun jiga da ke tafe a ranar Asabar mai zuwa.

Idan baku manta ba, a ranar 1 ga watan Maris ne aka tasa keyar Ado Doguwa zuwa magarkama bayan zaman kotu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

iiq_pixel