“Tana Jin Dadi”: Matashiya Ta Hasko Cikin Hadadden Gidan Iyayenta Dauke Da Motoci Masu Yawa a Bidiyo

“Tana Jin Dadi”: Matashiya Ta Hasko Cikin Hadadden Gidan Iyayenta Dauke Da Motoci Masu Yawa a Bidiyo

  • Wata matashiyar budurwa ta baje kolin tarin arzikin da Allah ya yi wa iyayenta yayin da ta dauki bidiyon cikin dankareren gidansu
  • Ganin hadaden harabar gidansu da motocin da ke ciki, mutane da dama sun magantu kan auren mahaifiyarta duk da ta ce auren hadi ne
  • Cike barkwanci, mutane da dama a sashin sharhi sun tambayeta ko mahaifinta na da abokai masu dukiya da suka shirya aure

Wata matashiya yar Najeriya ta baje kolin arzikin iyayenta a cikin wasu bidiyoyi guda biya. A bidiyon farko, ta bayyana cewa mahaifiyarta ta fada masu cewa auren hadi aka yi mata da mahaifinsu.

Mutane da dama da suka ga irin dukiyar da ahlin ke da shi da manyan motoci da dama a garejin motarsu sun ce za su so kasancewa a irin wannan auren na hadi.

Kara karanta wannan

“Ban San Haka Aure Yake Ba”: Matashiya Ta Fashe Da Kuka, Ta Ce Ba Za Ta Sake Aure Ba

Budurwa da hadaden gidan alfarma da mota
“Tana Jin Dadi”: Matashiya Ta Hasko Cikin Hadadden Gidan Iyayenta Dauke Da Motoci Masu Yawa a Bidiyo Hoto: @bellakiss022
Source: TikTok

A bidiyonta, ta dan zagaya da mutane cikin hadadden gidansu da dirka-dirkan kujeriu na alfarma. Da ganin cikin gidan za ka san cewa an narka dukiya a wajen.

An shirya fitilun cikin gidan da kyau inda ya dace da farin fentin jikin bangon. An manna hoton iyalin a wurare daban-daban na bangon gidan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kalli bidiyon a kasa:

Ga daya biyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

Ifeaks ta ce:

"Dan Allah ina bukatar wanda ya hada wannan aure dan Allah ya hada aurena nima."

clintonalex6 ta ce:

"Uwata za ta kashe ni idan na yi mata irin haka amma ita ma ta aure mahaifina ne auren hadi."

Debby ta ce:

"Wannan ba rangadi bane, faluka biyu kawai kika nuna mana da matattakalar bene."

Preetypranky ta ce:

"Mahaifiyarki ce kawai za ta bani shawara a rayuwar nan na karba wakar nan ya ban dariya rayuwar nan sharholiya ce."

Kara karanta wannan

Rudani: Tashin hankali yayin da aka tsinci gawar mata da danta a cikin wani gida a Kano

Walkingtalkinggoddess ta ce:

"Dan Allah ki kawo wannan mai dalilin auren ya hada namu."

Aaliyah Omololu ta ce:

"Ku shirya mun aurena fa."

Ni da aure sai a lahira: Budurwa ta koka, ta ce ba za ta sake aure ba

A wani labarin kuma, wata matashiya mai suna Bella a TikTok ta sharbi kuka da hawaye kan halin da take fuskanta a gidan aurenta inda ta ce ba za ta sake yin aure ba a rayuwarta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng