'Yan Siyasa Na Son Shigo Da Ƴan Daba Domin Kawo Rikici Ranar Zaɓe, Rundunar Ƴan Sandan Kano

'Yan Siyasa Na Son Shigo Da Ƴan Daba Domin Kawo Rikici Ranar Zaɓe, Rundunar Ƴan Sandan Kano

  • Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta fallasa wani shiri da wasu ɓata garin ƴan shiyasa ke shiryawa a jihar
  • Rundunar ƴan sandan ta bayyana cewa akwai wasu ɓata gari dake son shigo da ƴan daba cikin jihar
  • Sai dai rundunar ta bayyana cewa ba zata yi ƙasa a guiwa ba wajen ganin ta hukunta duk wasu ɓata gari

Jihar Kano- Rundunar ƴan sandan jihar Kano, a ranar Litinin ta tona wani shiri na wasu ɓata garin ƴan siyasa a jihar na son shigo da ƴan daba domin tayar da hargitsi a zaɓen gwamnoni dake tafe ranar Asabar. Rahoton Vanguard

Yan Sanda Kano
'Yan Siyasa Na Son Shigo Da Ƴan Daba Domin Kawo Rikici Ranar Zaɓe, Rundunar Ƴan Sandan Kano Hoto: Kano Focus
Asali: UGC

Kwamishinan ƴan sandan jihar, CP Mamman Dauda, wanda bankaɗo wannan shirin a cikin wata sanarwa ta hannun kakakin rundunar ta jihar, SP Abdullahi Haruna, ya gargaɗi ƴan daba da masu neman tayar da fitina,

Kara karanta wannan

Kisan Ɗan Gwamna Wike: Daga Ƙarshe Gaskiya Ta Fito Fili

Da su ƙauracewa jihar ko kuma su fuskanci hukunci mai tsauri. Rahoton Tribune

Haruna ya bayyana cewa rundunar zata haɗa hannu da sauran jami'an tsaro a jihar domin tabbatar da cafkewa da hukunta duk masu aikata wannan laifin.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A kalamansa:

Rundunar ƴan sandan jihar Kano a ƙarƙashin jagorancin CP Mamman Dauda, ta samu bayanin cewa wasu ɓata garin ƴan siyasa suna shirin shigo da ƴan daba cikin jihar da niyyar kawo hargitsi,
"A zaɓen gwamna dana ƴan majalisar dokokin jiha na ranar Asabar, 11 ga watan Fabrairun 2023."
“Kwamishinan ƴan sandan yana gargaɗi ga ƴan daba, masu tada rikici da duk wasu ɓata gari kan su kiyayi jihar domin rundunar ba zata yi ƙasa a guiwa ba wajen ganin ta hukunta duk wasu masu neman taɗa rigima."
“Rundunar tare da haɗin guiwar sauran hukumomin tsaro a jihar zata tabbatar da cafkewa tare da hukunta duk waɗanda ake zargi. Sannan kuma za a miƙa ƴan daban tare da waɗanda ke ɗaukar nauyin su tare zuwa kotu." 

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: An Kama Ɗan Majalisar Tarayya Na NNPP da Bindiga a Kano

“Muna so muyi amfani da wannan damar domin miƙa godiya ga mutanen jihar Kano bisa goyon bayan da suka bamu lokacin zaɓen shugaban ƙasa dana ƴan majalisun tarayya wanda aka gudanar cikin zaman lafiya.
“Kwamishinan yana son al'ummar jihar su cigaba da tafiya akan wannan turbar domin mun samu zaɓe wanda babu rigima ko kaɗan a cikin sa."

Malamai Sun Yi Wa Gwamna Addu'a Yayin da Mambobin PDP Suka Koma APC

A wani labarin na daban,.malaman musulunci sun yiwa gwamnan jihar Kwara adduar samun nasara.

Haka kuma wasi dubunnan mambobin jam'iyyar PDP sun koma.APC a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng