“Da Daddare Za Ka Kashe Kudin”: Matashi Ya Yi Amfani Da Keken Dinki Wajen Dinke N100
- Wani bidiyo da ya yadu a TikTok ya nuno wani dan Najeriya da ya yi amfani da keken dinki wajen dinke N100
- Takardar N100 ya yage kuma a bayyane yake baya so ya jefar da kudin don haka ya hada ya dinke
- Dan gajeren bidiyon da ya nuno shi yana dinke kudin ya haifar da martani masu ban dariya daga yan TikTok
Wani dan gajeren bidiyo da aka gano a TikTok ya nuno wani mutum da ya yi amfani da da keken dinki wajen dinke yagaggen N100.
A bidiyon, mutumin wanda ke zaune kan keken ya fara nuno N100 wanda ya rabu gida biyu.
Kamar kwararren tela, mutumin ya dinke kudin kamar yadda ake dunka zanin atampa.
Bidiyon matashi yana dinke N100 ya yadu
Lokacin da ya gama dinke kudin, wajen da aka dinke ya dan yanmutse.
Sakamakon Zaben 2023: A Karshe Babban Sarkin Yarbawa Ya Magantu Kan Soke Zabe Da Obasanjo Ya Ce A Yi
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Tuni bidiyon ya yadu kuma ya haifar da martanoni masu ban dariya daga yan Najeriya da dama. Wasu sun ce babu wanda zai karbi kudin daga hannunsa.
A sashin sharhi, ya ce ya gaza kashe kudin bayan ya dinke inda ya yage kamar zani. Shafin @drenati01 ne ya wallafa bidiyon.
Kalli bidiyon a kasa:
Jama'a sun yi martani
@uwegbe_olose ta ce:
"Kada ka kusanci shagona da shi."
@user3023164218260 ya yi martani:
"Da daddare za ka kashe shi."
@ONYI 001 ta ce:
"Kada ka dauki kudin ka zo kusa da shagon mahaifiyata."
@sheIsOmoolawealth ya ce:
"Ka yi amfani da shi wajen siyan tsire da daddare."
@Maryham— ta ce:
"Tunani mai kyau babu karamin kudi a kasar nan kuma."
@Ayomhide123 ta yi martani:
"Da daddare za ka kashe shi."
@Pamilerin Balogun ya ce:
"Kada dai ka yi amfani da shi wajen shiga motana saboda lokacin ne za ka san cewa bana siyan man fetur na N100."
@haleemah 18 ta ce:
"Shima ka dinke shi da zare kalansa."
Chajin POS ya ruguzo da 90% saboda hukuncin kotun koli
A wani labari na daban, mun ji cewa hukuncin da kotun koli ta yanke na ci gaba da amfani da tsoffin N200, N500 da N1000 ya sanya kudin da masu POS ke chaji yayin cire kudi ya ruguzo sosai.
Asali: Legit.ng