Yan Sanda Sun Sheke Yan Bindiga Biyu a Musayar Wuta a Jihar Bauchi
- Jami'an tsaro sun yi nasarar dakile harin garkuwa da mutane a garin Rafin Gora, ƙaramar hukumar Ningi a jihar Bauchi
- Kakakin yan sandan Bauchi, SP Ahmed Wakil, ya ce dakaru sun sheke biyu daga cikin maharan yayin artabu
- Ya ce a halin yanzun sun ceto wanda suka yi yunkurin sace wa kuma jami'ai sun bazama farauto yan ta'addan
Bauchi - Rundunar 'yan sanda ta jihar Bauchi ta halaka wasu yan bindiga 2 da ake zargin masu garkuwa ne a Rafin Gora, karamar hukumar Ningi ranar Jumu'a, ta ceto mutum ɗaya.
Jaridar Punch ta tattaro cewa jami'in hulɗa da jama'a na rundunar yan sandan jihar, SP Ahmed Wakil, ne ya tabbatar da haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi.
Ya ce maharan sun kutsa gidan wani mazaunin garin Rafin Gora kuma suka yi yunkurin sace ɗansa ɗan kimanim shekara 28 a duniya.
Kakakin 'yan sandan ya ce:
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
"Matashin ya masu turjiya yayin da suka yi yunkurin tafiya da shi kuma sanadin haka ne suka harbe shi gefen cikinsa sa'ilin da ya yi yunkurin guduwa."
"Nan da nan dakarun yan sanda da haɗin guiwar 'yan bangan yanki suka shirya kuma suka kai ɗauki wurin, suka fuskanci masu garuwan waɗanda suka musu maraba da ruwan wuta."
SP Wakil ya kara da cewa ba tare da bata lokaci ba jami'an tsaron suka maida martani, aka yi musayar wuta wanda ya tilasta wa maharan tserewa da raunukan harsashi.
Vanguard ta rahoto Ahmed Wakil na cewa
"A nan biyu daga cikinsu suka sheƙa barzahu kuma jami'ai sun kwato bindiga kirar AK-47. Tuni aka kwato wanda suka so sacewa kuma an garzaya da shi Asibitin tarayya da ke Birnkn Kudu domin yi masa magani."
Kakakin yan sandan ya ci gaba da cewa jami'ai sun bazama farautar maharan da suka tsere da nufin damƙo su domin doka ta yi aiki a kansu.
An Harbe Wani Basarake Har Lahira a Jihar Kano
A wani labarin kuma Yan bindiga sun kutsa har cikin gidan, sun kashe mahaifin shugaban ƙaramar hukuma a Kano
Rahotanni sun nuna cewa maharan sun shiga gidan Dagacin kauyen Maigari, karamar hukumar Rimin Gado, sun harbe shi har lahira
Marigayin ya kasance mahaifin shugaban karamar hukumar Rimin Gado, Barista Munir Dahiru Maigari.
Asali: Legit.ng