Yan Daba Sun Kai Farmaki Cibiyar Tattara Sakamakon Zabe A Bauchi
- Wani gungun yan daba sun kai hari cibiyar tattara sakamakon zabe tare da raunata mutane da dama
- Jam'iyyar PDP ta ce an kori yan jam'iyyar daga cibiyar tattara sakamakon zaben tare da gabatar da sakamakon karya
- Tuni dai jam'iyyar ta PDP da dan takararta suka yi watsi da sakamakon zaben inda zasu kalubalanci rashin nasarar ta su a kotun
Bauchi - Rahotanni sun bayyana yadda aka yi wa mutane da dama rauni biyo bayan harin da wasu gungun yan daba suka kai cibiyar tattara sakamakon zaben Bogoro/Dass/Tafawa Balewa a garin Bununu da ke Jihar Bauchi.
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa an lalata motoci sama da goma wanda mafi yawanci mallakar yan jam'iyyar PDP me mulki a jihar.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Wani tsohon mai taimakawa Yakubu Dogara kan harkokin watsa labarai, tsohon shugaban majalisar tarayya, Iliya Habila ne ya bayyana haka ga yan jarida a wata tattaunawa da yan jarida ranar Juma'a.
Ya bayyana cewa da kyar ya tserewa yan daban wanda suke dauke da mugayen makamai.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC ta bayyana dan takarar APC, Ja'afar Leko, a matsayin wanda ya lashe zaben inda ya kayar da na PDP, Kefas Magaji.
Leko ya samu goyon bayan Dogara wanda ke wakiltar yankin karo na hudu a majalisar.
A cewarsa:
''A matsayina na dan jam'iyyar PDP kuma daya daga cikin magoya bayan Kefas Magaji, mun zo ne don ganin yadda ake tattara sakamakon, kwatsam sai muka ga an kawo yan daba Bununu.
''Mun yi mamakin yaddda aka dauke cibiyar daga Zwall zuwa Bununu. Daga baya da yammaci, sai muka fahimci dalilin (dauke cibiyar tattara sakamakon) don a kawo rudani a kuma basu damar aiwatar da sharrin da suka yi niyya.
''Tsahon awanni, sun tsare ma'aikatan zabe, tsahon awanni sun hana jami'an tsaro aiki, daga can kuma a makarantar firamare, inda suke a boye suka fara gudanar da ta'addanci."
Ya cigaba da cewa:
''A takaice, sai da jami'an sojoji suka shiga lamarin kafin su hada sakamakon karya. Sun fara ta'addanci akan duk wanda suka fuskanci ba nasu bane. Nima da kyar na sha a hannun yan daban.
''Bayan sun Kori da yawa daga cikin magoya bayan mu, sun san yanzu abu ne mai sauki su bayyana sakamakon karya. A takaice, sai 1:00 na dare suka sanar da sakamakon zaben ranar Litinin a munafince wanda haka ba abin amincewa bane. An mana kwacen nasara, shi ya kamata a sanar a matsayin wanda yayi nasara, amma an mana fashi da rana tsaka."
Dan takarar PDP, tsohon mai bawa gwamnan Bauchi shawara kan harkokin shari'a ya yi watsi da sakamakon, inda ya ce zai kalubalanci rashin nasarar ta shi a kotu.
Asali: Legit.ng