Abin Ban Takaici Cocin Gidan Gwamnati Ta Asoroko Za'a Rufe ta Na Tsawon Shekara 4 - Okowa

Abin Ban Takaici Cocin Gidan Gwamnati Ta Asoroko Za'a Rufe ta Na Tsawon Shekara 4 - Okowa

  • Saboda takarar da jam'iyyar APC mai mulki ta bayar na Musulmi Musulmi, Okowa ya nuna fushin sa da cewa, za'a rufe babbar cocin Aso rock
  • Okowa yace gwamnatin tarayya a karƙashin jam'iyyar APC, ta tafka maguɗi a zaɓen shugaban kasa daya wuce wanda yayi sanadiyyar faɗuwarsa
  • Ya yi Kira da Al'ummar Kirista Su Goma Ga Allah A daidai wannan lokaci na jarabawa

Bayan sanar da sakamakon zaɓen da aka gudanar satin daya wuce na shugaban ƙasa dana ƴan majalisun tarayya, ra'ayi na cigaba da kwarara.

Biyo bayan shan kaye da jam'iyyar PDP da LP sukayi a hannun jam'iyya mai mulki ta APC.

Ɗaya daga cikin sanannu da suka yi shura a zaɓen daya gaba, Ifeanyi Okowa , mataimaki ga Atiku Abubakar ya ɓara cikin ɓacin rai da jimami.

Kara karanta wannan

An Dakatar da Shugaban Jam'iyyar APC a Neja Bisa Zargin Dangwalawa Atiku Kuri'a

Okowa
Abin Ban Takaici Cocin Gidan Gwamnati Ta Asoroko Za'a Rufe ta Na Tsawon Shekara 4 - Okowa Hoto: Legit.ng
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Gwamnan na jihar Delta, yayi korafi a kan cewa, ba haka aka so ba ace wai za'a kulle babbar cocin dake cikin fadar shugaban kasa ta Ado Rock saboda tikitin da APC ta bayar na musulmi da Musulmi a zaɓen daya gabata.

Okowa yayi wannan batu ne a wani taro da yayi da ilahirin shugabancin wata babbar coci mai suna "God's Fountain of Life Mission" a gundumar Oleh dake ƙaramar hukumar Isoko South ta jihar..

A cewar Okowa:

" Na tabbatar da cewa, wannan lokaci ne da zamu koma ga Ubangiji, mu tabbatar da abinda yake so shi mukayi a jihar mu da najeriya. Lokaci ne da zamu ƙara imanin mu bawai mu dinga fushi ba. Muyi ta addu'a, kuma muyi tunani na cikin zuciya.

Da yake tofa albarkacin bakinsa akan yadda zaɓukan ranar Asabar ɗin data gabata ya kasance, Okowa yace, zaɓen ya haɗu da tasgaro wanda hakan ke nufin an canja asalin sakamakon yadda ya kamata ya kasance.

Kara karanta wannan

Yan Boko Haram Yunwa Da Hare-Hare Yasa Sun Koma Sace Mutane Tare Da Neman Kudin Fansa

Okowa yace:

"Mundai ga yadda akayi maguɗi tare da lalata sakamakon zaɓen....". Inji shi.

Okowa ya hori shuagabancin addini dana jama'a dasu tabbatar sun zabi jam'iyyar sa a zaɓe mai zuwa.

Jaridar Leadership ta ruwaito yadda Okowa ya kuma godewa haɗakar majami'un abisa bashi dama da sukayi yayi musu magana.

Yan Kasuwa Da Direbobi Na Cigaba Da Kin Karbar Tsohon Kudi Duk Da Umarnin Kotun Koli

Binciken jaridar Legit ya gano cewar masu sana'o'i da kuma direbobi a kwaryar birnin Legas na cigaba da kin karbar tsohon kudin tare da bayyana cewa sai sun ji amincewar Shugaba Muhammadu Buhari kan hukuncin kotun.

A sabon hukuncin da kotun kolin ta yanke ranar Juma'a, kotun kolin ta ce tsohon kudin zai cigaba da zama halastacce har zuwa 31 ga watan Disambar 2023, tare da yin watsi da sauya fasalin takardun kudin.

Kotun kuma ta ce ba a bai wa mutane isasshen wa'adi ba idan akayi la'akari da sashe na 20 na kudin dokar CBN na 2007.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida