"Ji Nake Tamkar Ina Cikin Aljanna" Inji Mutumin Daya Auri Mata Biyu Rigis Lokaci Daya A Jihar Niger

"Ji Nake Tamkar Ina Cikin Aljanna" Inji Mutumin Daya Auri Mata Biyu Rigis Lokaci Daya A Jihar Niger

  • Umar yace Dalilin Auren Sa Bai Rasa Nasaba da Yadda Yaga Baban Sa ya Auro Mata Huɗu, Kuma Suna Zaune A Cikin Salama Da Zaman Lafiya.
  • Tun Daga Nan Umar Yace Zaiyi Aure Fiye Da Ɗaya, Watakila Ma Uku Ko Huɗu Zai Aura Duk A Rana Guda Indai Da Hali Kamar Yadda Yace.
  • Umar Ya KarKare da Cewa, Auren Nan da Yayi Ji Yake Tamkar Yana Cikin Tafkin Alkausara ko Kuma Yana Cikin Lambu A Aljannar Firdausi.

Aure yaƙin maza, wani lokacin ma har matan na tsoron sa, duk da tarin ni'imomi da falala dake cike dashi aru aru.

Maza na tsoron shine idan basu da halin hidindimu dake tattare dashi wajen gudanar da shagulgulan auren.

Yayin da a ɗaya ɓangaren, mata na tsoron shine saboda fargabar barin gidajen iyaye domin yin rayuwa tare da masoyansu.

Kara karanta wannan

Yan Sanda Sun Cafke Ɓarayi 50 da Suka Sace Kaya a Gobarar Kasuwar Maiduguri.

Auren Mata Biyu
"Ji Nake Tamkar Ina Cikin Aljanna" Inji Mutumin Daya Auri Mata Biyu Rigis Lokaci Daya A Jihar Niger Hoto: DailyNigerian
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Amma shi Umar Sani ba haka take ba a wajen sa, domin da alama bai haɗu da irin wannan ƙalubalen ba.

Hakan na zuwa ne, yayin da matashin ya auri mata biyu kuma ya tare da abinsa a rana guda a can birnin Minna dake jihar Niger.

Saboda daɗin aure da kulawa da matashin yake fuskanta, cewa yayi shi auren nan ma da yayi jinsa yake kamar yana cikin tafkin alkausara ko aljanna.

Shi dai Umar, an ruwaito cewar ya auri sahibar sa Safina da Maryam ne a ranar juma'a kamar yadda ya faɗawa wata jarida dake gabatar da shirye-shiryen ta a yanar gizo gizo mai suna Tsalle Ɗaya.

Inda ya ce:

"Haƙiƙa ji nake tamkar ina ninƙaya a cikin aljanna, tabbas ina matuƙar godiya ga Ubangiji Allah , domin farin ciki na bazai misaltu ba." Inji shi.

Kara karanta wannan

Yan Watanni Bayan Rabuwa Da Matarsa Da Kuma Musulunta, JJC Skillz Yayi Aure A Kano

"Na godewa Allah sosai abisa auren matan nan guda biyu danayi. Dukkan su, suna da fahimta, abin godiya ne wannan.

Sannan Umar ya cigaba da cewa:

"Mutane da yawa na ganin auren ka iya zuwa da matsala daga gurin matan, amma ban samu wata matsala daga gurin kowacce saboda Allah yasa komai yazo yadda nake son shi."

Umar ya ƙara da cewa, yin auren matan biyun da yayi rigis a lokaci guda nada alaƙa akan yanayin gidan su daya taso, inda yace, su daman gidan su ana auren mata fiye da ɗaya.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito Umar na cewa:

"Tun ina da shekaru goma naga babana da mata huɗu, kuma suna rayuwar su cikin salama. Tun daga nan nayiwa kaina alƙawari nima zanyi aure fiye da ɗaya, watakila ma uku ko huɗu zan aura duk a rana guda indai da hali".

Kara karanta wannan

"Tinubu Na Iya Soke Dokar Sauya Fasalin kudin Naira na CBN A Satin Sa Na Farko a Ofis" Masani

Duk da haka, iyayen sa sunyi mamaki lokacin da suka ji labarin hakan. Amma kuma basu tsaida shi ba, wajen cika mafarkin sa.

Ya ƙarkare da:

"Iyaye na sunyi mamaki sosai, hattana babana bai zata zan iya auro mata biyu a lokaci daya ba. Duk da haka basuyi sa-in-sa da abinda nazo dashi ba. Abu mafi mahimmanci gare su shine, mu samu gida mai cike da zaman lafiya da lumana. Inji Umar.

CBN Ya Yi Gum Game da Hukuncin da Ƙotun Koli Ta Yanke Kan Sauya Naira

A wani abu mai ban mamaki, har yau Babban bankin Najeriya (CBN) ya yi gum da bakinsa bai ce komai ba har zuwa yanzun bayan Kotun ƙoli ta umarci a ci gaba da hada-hada da tsoffin takardun N200, N500 da N1000 har zuwa 31 ga watan Disamba, 2023.

Wani babban jami'inbabban bankin daya zanta da manema labarai da aka boye sunan sa yace bankin yana aiki ne bisa sahalewar bangaren zartaswa.

Wannan kalamai na nufin CBN ka iya wanke hannunsa ya miƙa nauyin jawabi kan batun sauya fasalin naira zuwa hannun gwamnatin tarayya.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida