Yan Kasuwa Da Direbobi Na Cigaba Da Kin Karbar Tsohon Kudi Duk Da Umarnin Kotun Koli

Yan Kasuwa Da Direbobi Na Cigaba Da Kin Karbar Tsohon Kudi Duk Da Umarnin Kotun Koli

  • Biyo bayan umarnin kotun koli na cigaba da karbar tsohon kudi, wasu yan kasuwa sun ce ba za su amince da tsohon kudin ba
  • Yan kasuwar sun bayyana cewa za su cigaba da karbar tsohon kudin ne kawai bayan amincewar gwamnatin tarayya ko babban bankin kasa ga umarnin kotun koli
  • Ana fargabar ko kotun koli da gwamnatin tarayya za su amince da umarnin kotun na tsawaita karbar tsohon kudi har zuwa karshen shekara

Legas - Duk da umarnin kotun koli kan tsohon kudi, Daily Sun ta binciko yadda masu sana'o'i da kuma direbobi a kwaryar birnin Legas ke cigaba da kin karbar tsohon kudin tare da bayyana cewa sai sun ji amincewar Shugaba Muhammadu Buhari kan hukuncin kotun.

Tun da farko kotun kolin ta yi umarnin cewa a cigaba da karbar tsohon kudi har zuwa 31 ga watan Disambar 2023, inda ta yi watsi da wa'adin babban bankin kasa CBN.

Kara karanta wannan

Kashe tsoffin Naira: CBN ya yi maganar da kowa ya kamata ya sani kan hukuncin kotu

Takardun Kudi
Takardun Kudin Najeriya. Hoto: The Sun
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sai dai, a sabon hukuncin da kotun kolin ta yanke ranar Juma'a, kotun kolin ta ce tsohon kudin zai cigaba da zama halattace har zuwa 31 ga watan Disambar 2023, tare da yin watsi da sauya fasalin takardun kudin.

Kotun kuma ta ce ba a bai wa mutane isasshen wa'adi ba idan akayi la'akari da sashe na 20 na kudin dokar CBN na 2007.

Bisa wannan dalili, babban bankin kasa zai tsawaita halaccin kudin zuwa 31 ga watan Disamba, 2023, bisa dalilin cewa kasashe da dama suna barin sabo da tsohon kudi su zagaya a tare akalla na shekara guda.

Idan za a iya tunawa a Disambar 2022, babban bankin kasa CBN ya sanar da sauya fasalin N200, N500 da kuma 1,000 daga 10 ga watan Fabrairu 2023.

Dalilin haka, gwamnonin kasar 16 suka nuna rashin amincewa da dokar, tare da shigar da karar gwamnatin tarayya, su na rokon kotun da ta dakatar da dokar.

Kara karanta wannan

Masu Sayar Da Hatsi a Kasuwannin Abuja Bayyana Dalilin Da Yasa Ba Su Karban Tiransifa, Sai Tsabar Kudi

Kotun kolin ta yi hukunci bisa abin da gwamnonin suka bukata, tana mai dakatar da gwamnatin tarayya daga wa'adin 10 ga Fabrairu.

Amma akwai rashin tabbacin ko kotun na da ikon yin hukuncin, kamar yadda ake ganin ko babban bankin kasa, ma'aikata mai zaman kanta, zai bi umarnin kotun tun da shi aka shigar kara ba.

A baya bayan nan, gwamnatin tarayya ta sanya sabon wa'adi, inda ta amince da karbar tsohuwar N200 har na tsawon Karin kwanaki 60.

Shugaba Buhari ya bayyana a wata hira da cewa CBN sun dauki matakin sauya fasalin kudi bisa umarnin sa.

Duk da cewa, hukuncin kotun na ranar Juma'a abu ne da aka dade ana jira don saukaka al'amura, sai dai, a wasu wuraren kasuwanci kamar Ajah, Orile, Alaba sun ce ba za su karbi kudin ba har sai sun jira babban bankin kasa CBN ko gwamnatin tarayya sun fitar da sanarwar amincewa da hukuncin duk da bayanin da kotu ta yi na cewa ba za a iya fasa canja kudin ba biyo bayan ganawar sirri da gwamnan babban bankin kasa.

Kara karanta wannan

Sabuwar Matsala Ta Bullo Yayin da Bankuna Suka Fara Zuba Tsoffin N500 da N1000 a ATM

Emeka Felix, wani mai siyar da kayan wutar lantarki, ya ce ''an riga an shiga wani hali sai kuma ga wannan hukunci na kotun koli. Ba na tunanin Najeriya tana cikin hayyacinta."

Yanzu mu abin dariya ne a sauran kasashen duniya. Gwamnati ta gaza. Zan cigaba da karbar kudi ta asusun bankina don gudanar da kasuwanci na.

Shima a nasa jawabin, Eze Calistus, wani direba, ya ce ba zai karbi tsohon kudi daga hannun fasinja ba saboda an riga an dade ba a karba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164