Babban Magana: Kungiya Ta Bukaci Jami'an Tsaro Su Kama Shugaban INEC, Mahmoud Yakubu Kan Zaben 2023
- Wata kungiya ta mazauna Edo ta bukaci jami'an tsaro su cafke shugaban hukumar zaben Najeriya, Farfesa Mahmoud Yakubu, kan saba dokoki yayin zaben ranar 25 ga watan Fabrairu
- Kungiyar ta yi ikirarin cewa hukumar ta INEC ta yaudari yan Najeriya domin ta fada musu za ta aika sakamakon zabe kai tsaye ta hanyar amfani da BVAS amma ba ta yi hakan ba
- A sanarwar da ta karanto yayin taron manema labarai, kungiyar ta yi kira ga sauran yan Najeriya su fito su yi Allah wadai da zaben da INEC ta yi da ta kira fashi da rana tsaka
Edo - Wata kungiya mai suna 'Concerned Edo Citizen Forum' ta yi kira ga hukumomin tsaro har da DSS su kama shugaban hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, Farfesa Mahmoud Yakubu, The Sun ta rahoto.
Kungiyar na son a kama Yakubu ne kan abin da ta kira jefa kasa cikin fitina bisa yadda ta yi babban zaben 2023 wanda ta yi ikirarin bai cika ka'ida ba musamman na dokar zaben 2023 wacce ta yi magana kan tura sakamakon zabe kai tsaye zuwa ma'ajiya ta hanyar amfani da BVAS.
Kungiyar ta yi wannan kiran ne yayin wani taron manema labarai da ta kira a Birnin Benin don yin Allah wadai da zaben ranar 25 ga watan Fabrairu, da ta kira fashi da rana tsaka, tana zargin INEC da saba dokokin dimokradiyya.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Da ya ke karanta sanarwar manema labarai mai dauke da sa hannun direktan watsa labarai na kungiyar, Kwamared Osas Felix Osagie ya ce:
"INEC ta yi aiki da gaske kuma ba tare da kunya ba don dakile ka'idojin dimokradiyya don haka, a matsayinta na hukuma dole a yi karar ta.
Zaben 2023: Kungiyar ANA Ta Taya Tinubu Murna, Ta Gargadi Obasanjo Kan Yi Wa Dimokradiyya Zagon Kasa
"INEC ta rude yan Najeriya da BVAS saboda ta fada mana fiye da sau 100 cewa za a tura sakamako kai tsaye zuwa rumbin ajiyar bayanai na INEC, amma mun sha mamakin, yadda INEC ta saba wannan ka'ida, ba za a amince da wannan zaben ba don ya saba ka'idojin dimokradiyya.
"Don haka mun kira ga hukumomin tsaro a matsayin batun gaggawa su kama shugaban INEC."
Kungiya ta yi kira ga kotu ta yi adalci
Kungiyar ta kuma yi kira ga bangaren shari'a ta yi aikinta da tsoron Allah saboda abin da ya faru a Najeriya ba zai iya faruwa a duniyar dabobbi ko na shaidanu ba.
Ta kuma yi kira ga sauran yan Najeriya su fito su yi Allah wadai da sakamakon zaben su kuma nuna rashin yardansu.
Asali: Legit.ng