An Gurfanar da Matasa Bisa Zargin Karya Kofar Shagon Siyayya Na Shoprite a Ibadan
- An gurfanar da wasu matasa a gaban kotu bisa zarginsu da fasa kofar kantin siyayya na Shoprite a jihar Oyo
- Wannan lamarin ya zo da tsaiko, domin a baya sun bayyana za su biya, amma kuma suka ki cika alkawari
- An ba da belinsu tare da cewa su nemi wanda zai tsaya musu, kana aka dage ci gaba da sauraran karar
Ibadan, jihar Oyo - An gurfanar da wasu matasa; Tunde Okunuga mai shekaru 33 da kuma John Solomon bai shekaru 19 a ranar Alhamis a kotun majistare da ke Iyaganka a Ibadan bisa zargin lalata gilashin kofar shagon siyayya na Shoprite da Ring Road a Ibadan.
Wadanda aka gurfanar din da ba a bayyana sunayensu ba suna fuskantar laifukan hada baki, barna da kuma karya a gaban kotu.
Sai dai, da aka karanto musu laifukansu, dukkansu sun musanta zargin da ake musu, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.
Sun ki biya bayan sun yi barna
Mai gabatar da kara, Mr. Philip Amusan ya shaidawa kotun cewa, matasan sun aikata laifin ne a ranar 26 ga watan Disamban 2022 da misalin karfe 8:41 na dare.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Amusan ya bayyana zargin cewa, wadanda ake karan bayan sun lalata kofar, sun dauki alkawarin gyara ta a gaban kotun kostomare Grade C na Ibadan.
A cewarsa, sun ki zuwa domin cika abin da aka yanke musu na gyara, don haka aka kawo su gaban wannan kotu ta majistare, kafar labarai ta Tori ta tattaro.
Sun saba dokar Oyo
Ya kuma bayyana cewa, laifukan da suka aikata sun saba da sashe na 516, 451 da 118 na kudin manyan laifuka na jihar Oyo, 2000.
Mai shari’a Mrs O. A. Akande na kotun majistare ta ba da belin wadanda ake zargin a kan kudi N50,000 tare da kawo mutum daya da zai tsaya musu.
Daga nan ne Akande ta dage ci gaba da sauraran karar zuwa ranar 5 ga watan Afrilu idan Allah ya kaimu.
A bangare guda, wani matashi aka kama a wani gari, inda yake kokarin sace janaretan kotu a lokacin da ake ci gaba da aiki dashi, kamar yadda rahotanni daga garin suka bayyanawa majiyar da muka samo.
Asali: Legit.ng