Basarake A Jihar Jigawa Da Yaransa 3 Sun Mutu A Hadarin Mota
- Allah ya yi wa Alhaji Muhammad Suleiman, dan Amar kuma Hakimin Basirka a Jihar Jigawa rasuwa
- Alhaji Suleiman ya rasu ne a ranar Alhamis tare da yayansa uku sakamakon hadarin mota a hanyarsu na zuwa Gwaram
- Abubakar Dutse, sarkin yakin Dutse ya tabbatar da rasuwar basaraken ya kuma ce za a yi masa jana'iza da yayansa a fadar sarkin Dutse
Dutse, Jigawa - Alhaji Muhammad Suleiman, dan Amar na Dutse kuma hakimin Basirka a jihar Jigawa ya riga mu gidan gaskiya.
Mai sarautar gargajiyar ya rasu tare da yayansa uku bayan motar da suke ciki ta yi hadari a kan hanyar Basirka Gwaram lokacin da suke hanyarsu ta zuwa garin Gwaram.
Matarsa da sauran yayansu biyu sun tsira daga hadarin, a cewar Sarkin Yakin Dutse, Abubakar Dutse, Daily Trust ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An tattaro cewa za a yi musu sallah jana'iza misalin karfe 2 na ranar Alhamis a fadar mai martaba sarkin Dutse.
Wakilin Legit.ng Hausa ya tuntubi wani wanda ke bibiyan harkokin fadar sarki wanda ya masa karin bayani dangane yadda hadarin ya faru.
Majiyar da ya nemi a sakaya sunansa ya ce a hanyar Basirka hatsarin ya faru kuma dutse motar tasu ta yi karo da shi.
Ya ce:
"Motar ta su ta bugi wani dutse ne sai kofar ta bude ta yi fatali da biyu daga cikin yaransa, sauran kuma motar da dungura da su cikin ruwa da ke kasar gadar da ke titin, hakan ya yi sanadin rasuwarsu."
Rasuwar Hakimin na Basirka na zuwa ne kimanin wata guda bayan rasuwar tsohon sarkin Dutse, marigayi Alhaji Nuhu Muhammad Sunusi wanda ya rasu a ranar 31 ga watan Janairu.
Abin da marigayi Sarkin Dutse Muhammadu Sanusi II ya fada wa Bola Tinubu kafin zaben 2023?
A wani rahoto a baya kun ji cewa marigayi Sarkin Dutse ya amince da cancantar zababben shugaban kasar na Najeriya ya jagoranci Najeriya duba da ayyukan da ya yi lokacin yana gwamnan Jihar Legas.
A yayin da Asiwaju Bola Tinubu ya kai wa marigayi Sarkin Dutsen ziyara a fadarsa, ya ce dan takarar shugaban kasar na APC ya taka muhimmin rawa don hada kan arewa da kudu don kafa jam'iyyar siyasa kakarfa.
Asali: Legit.ng