Kotu Ta Tasa Keyar Shugaban Masu Rinjaye a Majalisar Wakilai Zuwa Magarkama

Kotu Ta Tasa Keyar Shugaban Masu Rinjaye a Majalisar Wakilai Zuwa Magarkama

  • Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta gurfanar Hon. Alhassan Ado Doguwa bisa zargin hannu a kashe-kashe
  • An yi kashe-kashe a jihar Kano, inda aka ce akwai hannun dan majalisar wakilai kuma shugaban masu rinjaye
  • Ya zuwa yanzu, an tasa keyar dan majalisar zuwa magarkama har zuwa ranar 7 ga watan Maris mai zuwa

Jihar Kano - Kotun majistare a jihar Kano ta tasa keyar shugaban masu rinjaye a majalisar wakilai, Alhassan Ado Doguwa zuwa gidan yari.

Ana zargin dan majalisar ne da kitsa ayyukan ta’addanci da suka kai ga mutuwar mutane a lokacin zaben ranar Asabar 25 ga watan Faburairu.

An gurfanar da Doguwa ne a gaban kotun majistare na 58 da jihar Kano a ranar Laraba da yamma biyo bayan kwamushe shi a filin jirgin saman Malam Aminu Kano a ranar Talata.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: An Gurfanar da Ado Doguwa a Gaban Kotu, Babban Abinda Ake Zarginsa Ya Fito

An tura Ado Doguwa magarkama
Hon. Alhassan Ado Doguwa | Hoto: withinnigeria.com
Asali: UGC

Mai shari’a Ibrahim Mansur Yola ya ba da umarnin a tsare Doguwa ne bayan sauraran takardar rahoton binciken farko.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga nan, an dage ci gaba da sauraran karar zuwa ranar 7 ga watan Maris, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Yadda batun ya faro

A tun farko, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kano, SP Haruna Kiyawa ya ce, jami’ai sun kama Doguwa ne bisa zarginsa da kitsa ayyukan ta’addancin da suka tada hankali a Kano.

A cewar Kiyawa, da hannun Doguwa aka kashe wasu mutum uku tare da jikkata wasu takwas a karamar hukumar Tudun Wada a ranar 26 ga watan Faburairu.

Ya kuma bayyana cewa, an yi wannan barnar ne a lokacin da ake ci gaba da tattara sakamakon zaben shugaban kasa, kuma an ga bidiyo ya yadu kafar sada zumunta na yadda barnar ta kasance, Within Nigeria ta tattaro.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Yan Sanda Sun Cafke Alhassan Doguwa a Filin Jirgin Sama Na Kano

Kwamishina ya ce a binciki lamarin

A bangare guda, kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Muhammad Yakubu ya ba da umarnin a binciki lamari tare da kawo rahoto.

Hakazalika, ya ce bayan bincike ya kai ga gano zaren, an gayyaci Doguwa ya zo wurin ‘yan sanda, amma ya ki amsa gayyatar.

Wannan ne yasa aka kama shi a lokacin da yake shirin hawa a jirgi a filin jirgin saman Malam Aminu Kano da ke birnin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.