'Yan Bindiga Sun Kai Hari Ofishin Ƴan Sanda a Jihar Abia, Sun Yi Awon Gaba Da Makamai

'Yan Bindiga Sun Kai Hari Ofishin Ƴan Sanda a Jihar Abia, Sun Yi Awon Gaba Da Makamai

  • Miyagun ƴan bindiga sun kai wani hari kan ofishin ƴan sanda a jihar Abia a Kudancin Najeriya
  • Ƴan bindigan sun yi awon gaba da tarin makamai da wasu kayan aikin ƴan sanda a yayin harin
  • Tuni rundunar ƴan sandan jihar ta fara farautar waɗanda ake zargi da kai wannan mummunan harin

Abia- Ƴan bindiga a ranar Litinin sun kai hari ofishin ƴan sanda na Nkporo, a ƙaramar hukumar Ohafia ta jihar Abia, sannan suka kwashi makamai da yawa daga ofishin.

Ƴan bindigar sun dira a ofishin ƴan sandan ne cikin motoci ƙirar Sienna guda uku, suka farmaki ƴan sanda dake kan aiki sannan suka ɓalle ma'ajiyar makaman ofishin, suka sace bindiga ɗaya ƙirar AK-47 ɗauke da harsasai 30. Rahoton Punch

Jihar Abia
'Yan Bindiga Sun Kai Hari Ofishin Ƴan Sanda a Jihar Abia, Sun Yi Awon Gaba Da Makamai Hoto: The Cable
Asali: UGC

Waɗanda ake zargin sun kuma sun yi awon gaba da bindigun kwantar da tarzoma guda biyu da harsasai waɗanda har yanzu ba a san ko guda naea bane.

Kara karanta wannan

Dubu Ta Cika: Ƴan Sanda Sun Cafke Lakcara Ɗauke Da Na'urorin BVAS

Da yake tabbatar da aukuwar lamarin, kakakin hukumar ƴan sandan jihar, Geoffrey Ogbonna, a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, yace ƴan bindigar sun yi harbi kan mai uwa da wabi lokacin da suka kai hari a ofishin ƴan sandan.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Yayi bayanin cewa ƴan binigidan bayan sun tarwatsa ƴan sandan dake bakin aiki, sun shiga cikin ofishin sannan suka sace makaman. Ya ƙara da cewa rundunar su ta fara farautar waɗanda ake zargi dakai harin kan ofishin ƴan sandan

A kalamansa:

“Ɓata garin sun ɓalle ma'ajiyar makamai ta ofishin sannan suka sace bindiga guda ɗaya ƙirar AK 47 ɗauke da harsasai 30, bindigogin kwantar da tarzoma biyu da kuma harsasai waɗanda har yanzu ba a tantance adadin su ba."
"Sun kuma yi awon gaba da khakin ƴan sandan dake ajiya a ma'ajiyar da kuma waɗanda ke a jikin ƴan sandan dake a bakin aiki. Ƴan sanda uku sun samu raunika a harin"

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari Yayi Allah Wadai Da Kisan Ɗan Takara Ana Dab Da Zaɓe, Ya Ba Jami'an Tsaro Wani Umurni

A cewar Ogbonna, haɗin guiwar da ƴan sanda da sojoji suka ya sanya an gano mota ƙirar Toyota Sienna wacce aka gudu aka bari da wasu khaki, takalma da wasu kayayyaki a ciki. Rahoton The Cable

Rundunar Yan Sanda Ta Haramta Bukukuwan Da Zanga-Zanga Kan Zaben Shugaban Kasa a Kaduna

A wani labarin na daban kuma, rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ta haramta shagalin biki da zanga-zanga kan zaɓen shugaban ƙasa.

Rundunar ta kuma bayyana hukuncin da duk wanda ya karya dokar zai fuskanta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng