Yan Daban Siyasa Sun Kona Mutum Biyu Da Ransu a Ofishin NNPP a Kano

Yan Daban Siyasa Sun Kona Mutum Biyu Da Ransu a Ofishin NNPP a Kano

  • Wasu matasa sun rasa rayukansu a mutuwa mai zafi cikin ofishin jam'iyyar adawa ta NNPP a Kano
  • Hukumar yan sanda tace ta kashe dan daba daya kuma ta damke mutum hudu cikinsu
  • Kakakin hukumar Haruna Kiyawa yace ana gudanar da bincike kan wadannan hare-hare.

Kano - An kona wasu mutane da ransu yayinda rikicin bangar siyasa ya barke lokacin zaben shugaban kasa da yan majalisun tarayya a jihar Kano.

Hakazalika an kona ofishin jam'iyyar New Nigerian People’s Party (NNPP) dake karamar hukumar Tudun Wada dake Kano kurmus.

Kakakin hukumar yan sandan jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da wannan lamari, rahoton DailyTrust.

Kiyawa
Kakakin hukumar yan sandan jiha Kano Hoto: NTA/AIT
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kiyawa ya bayyana cewa haka aka kai hari ofishin hukumar zabe ta INEC dake karamar hukumar Takai ta jihar.

Kara karanta wannan

Karin bayani: 'Yan daba sun sa wuta a hedkwatar hukumar INEC a wata jihar Arewa

A cewarsa:

"An kona wasu mutum biyu dake cikin wata mota a cikin ofishin kamfen dan takarar majalisar wakilai na jam'iyyar NNPP kurmus har lahira."
"Hakazalika an yi kokarin kona ofishin INEC dake karamar hukumar Tudun Wada lokacin da wasu yan daba suka kai hari yayinda ake tattara kuri'u."

Kiyawa ya kara da cewa wasu yan bangan siyasan sun kai hari ofishin INEC dake karamar hukuma Takai amma jami'an tsaro suka dira wajen da wuri.

Yace:

"Yan daban bayan haka sun tare hanyar zuwa ofishin INEC amma jami'an tsaron da aka da wuri ya dakile yunkurin."
"Daya daga cikin yan sandan da aka jiwa rauni an garzaya da shi asibiti kuma daga baya ya mutu. An damke wasu mutum 4."

Kiyawa yace ana gudanar da bincike kan wadannan hare-hare.

Tirƙashi: Ɗan Acaɓar Da Ya Samu Nasarar Zama Ɗan Majalisa a Ƙarƙashin jam'iyyar Labor Party ta Peter Obi Ya Bada Mamaki

Kara karanta wannan

Yan Daba Sun Harbi Mata Biyu a Bayelsa Yayin da Rikcin Zabe Ya Kaure a Ribas

A wani labari, wani ɗan acaba a jihar ta Kaduna daya zama ɗan majalisa a ƙarƙashin jam'iyyar Labor party wacce Peter Obi yakewa takarar shugaban ƙasa.

Mutumin mai suna Mr Donatus Mathew, tuni baturen zaɓe ya sanar da lashe zaɓen da yayi na mazabar Kaura dake jihar Kaduna.

Da baturen zaɓen yake sanar da lashe zaɓen na ɗan Acaɓar, Farfesa Elijah Ella yace Mathew ya samu adadin ƙuriu guda 10,508 cicif.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida