Zaben 2023: Magoya Bayan Jam'iyyar Labour Na Barazanar Kashe Ni, Baturen Zaben Jihar Rivers Ya Koka

Zaben 2023: Magoya Bayan Jam'iyyar Labour Na Barazanar Kashe Ni, Baturen Zaben Jihar Rivers Ya Koka

  • Baturen zabe na Jihar Rivers ya koka kan yadda magoya bayan jam'iyyar Labour, LP, ke barazana ga rayuwarsa
  • Farfesa Charles Adias shugaban Jami'ar Tarayya ta Otuoke ya ce magoya bayan LP na zargin an kawo shi ne don a murde zabe
  • Ya bayyana cewa a matsayin sa na malami aikin sa shine ya hidimtawa kasa ya kuma koyar kuma ba zai bari a hada kai da shi a cuci kowa ba

Rivers - Baturen zaben Jihar zaben shugaban kasa na Jihar Rivers kuma shugaban jami'ar tarayya da ke Otuoke, Jihar Bayelsa, Farfesa Charles Adias, ya yi korafin cewa magoya bayan jam'iyyar LP na barazana ga rayuwarsa.

Adias ya ce tun bayan karbar aikin nasa, ya karbi sakonnin barazana bisa zargin an saka shi yin magudi a zabe, The Nation ta rahoto.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Zaben 2023: Obasanjo Na Son A Yi Wa Dimokradiyya Juyin Mulki, Kwamitin Kamfen Din APC Ta Yi Martani

Jami'in tattara zabe na Rivers.
Farfesa Adias ya ce magoya bayan LP na barazanar kashe shi. Hoto: The Nation
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Da ya ke bayani ga wakilin jam'iyyar LP na jiha, Deinye Pepple, lokacin tattara sakamakon zabe, a Port Harcourt, Adias ya ce ya aikinsa ba nuku nuku.

Kuma, ya ce aikinsa bashi da alaka da shigar da sakamakon zabe saboda shi yana karbar sakamakon da aka riga aka shigar daga wajen ma'aikatan zabe.

Pepple ya nuna rashin gamsuwa da wasu sakamakon amma ya yabawa baturen zaben kan sakamakon Ogba/Egbema/Ndoni, wasu kananan hukumomi a jihar bisa abin da ya kira sakamakon gaskiya.

A cewarsa:

''Duk sakamakon da ya gabatar yayi daidai da abin da yazo hannuna daga mazabu.''

Amma Adias ya ce:

''Ina ta daga kiran waya daga magoya bayan jam'iyyar ku. Ko da ina nan wajen wayata ta cika da sakonnin yan jam'iyyar ku suna barazanar kashe ni da sauran abubuwa.

Kara karanta wannan

Tsohon Gwamnan PDP Ya Caccaki Jam’iyya, Ya Jero Abin da Ya Jawo Masu Rashin Nasara

''Suna cewa wai nazo murde musu zabe. Ina bada shawara in kuna da wata matsala, ku koma akwatunan ku.''

Adias ya ce zai gudanar da aikinsa cikin kwarewa tare da kira da tunzurarrun magoya baya da su kai koke-kokensu inda ya dace.

Ya ce:

''A matsayin mu na malamai, aikin mu shine mu koyar kuma mu yi wa kasa hidima kuma shine abun da muke yi kuma zamu cigaba da yin aikin mu.''

Kwamishinan yan sanda mai kula da harkokin zabe a jihar Rivers, Adeoye Aderami, ya gargadi yan siyasa da magoya bayan jam'iyyu da su guji tada hankalin mutane don gudun tashin fitina.

Aderami ya yi Allah wadai da yada labaran karya a kafefen sada zumunta ya kuma shawarci mutane da su kiyayi irin labaran.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164