Jam’iyyar PDP Ta Tubure, Ta Ki Amincewa da Sakamakon da INEC Ta Fitar

Jam’iyyar PDP Ta Tubure, Ta Ki Amincewa da Sakamakon da INEC Ta Fitar

  • Jam'iyyar PDP ta bayyana rashin amincewarta ga yadda sakamakon zaben kasa ke fitowa, inda tace akwai bukatar a fahimci wasu abubuwa
  • A cewar PDP bai kamata a ce Bola Ahmad Tinubu na jam'iyyar APC ya fi Alhaji Atiku Abubakar na jam'iyyar ta PDP ba
  • A halin da ake ciki, an dakata da tattara sakamakon zaben wasu jihohin kasar saboda wasu abubuwan da ba a rasa ba

FCT, Abuja - Jam’iyyar PDP ta ki amincewa da sakamakon zaben shugaban kasa da hukumar zabe ta INEC ta fitar, Tribune Online ta ruwaito.

A cewar PDP, Atiku Abubakar, dan takararta na shugaban kasa ya samu kuri’u masu yawan da Bola Tinubu an APC bai samu ba.

Ta kuma bayyana cewa, duba da haka, bai kamata a ci gaba da tattara sakamakon zaben da aka jirkita ba.

Kara karanta wannan

Sakamakon Zaɓe: Tinubu da Atiku Sun Sha Kashi Hannun Peter Obi a Nasarawa

Wannan batu na PDP dai na fitowa ne daga cikin wata sanarwa da sakataren yada labaranta, Debo Ologunagba ya fitar.

Karin bayani na nan tafe...

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.