Jam’iyyar APC a Abia Ta Musanta Dakatar da Sanata Orji Kalu, Ta Ce Jita-Jitan PDP Ne
- Jam’iyyar APC a jihar Abia ya musanta jita-jitan dakatar da sanata Orji Kalu daga jam’iyyar saboda cin dunduniyarta
- An yada wani rahoto a yau Juma’a 24 ga watan Faburairu da ke cewa, APC ta dakatar da sanatan mai ci
- Wannan na zuwa ne kwana daya kafin yin zaben 2023 na shugaban kasa da ‘yan majalisun tarayya
Jihar Abia - Jam’iyyar APC a jihar Abia ta musanta labaran da ke yawo cewa, ta dakatar da sanatan Abia ta Arewa, Sanata Orji Uzor Kalu.
Da yake karyata batun, mai magana da yawun sanata, Okey Ezeala ya siffanta rahotannin da kitsawar jam’iyyar adawa ta PDP, Punch ta ruwaito.
A cewar sanarwar da ya fitar, jam’iyyar ta nesanta kanta da batun dakatar da sanatan, inda tace sam ba gaskiya bane.
Martanin APC ga rahoton da aka yada
Ezeala ya ce, duk shirin jam’iyyar PDP ne kasancewar ta fahimci za ta sha kaye a zaben da za a yi gobe Asabar 25 ga watan Faburairu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewarsa:
“Har yanzu Sanata Orji Uzor Kalu ne dan takarar jam’iyyarmu mai girma saboda jam’iyyar da mazabarsa sun gamsu da kokarinsa.”
Kasancewar rahoton ya ambaci cewa, Orji na ci dunduniyar jam’iyya, APC ta ce ba gaskiya bane, sanatan ya kasance dan jam’iyya mai tasiri kuma mai bin dokarta da oda.
Hakazalika, hadimin nasa ya kara da cewa, babu wata hujja da ke nuna Orji Kalu ya yiwa wani dan takarar da ba na APC kamfen.
Daga karshe, jam’iyyar APC ta bukaci magoya bayanta da daukacin al’umma da su yi watsi da dukkan rahotannin da ake yadawa na karya game da mambanta, kana ya bukaci al’umma da su fito su zabi ‘yan takararta.
Ta ina labarin dakatar da Orji Kalu ya fito?
A tun farko, an yada labarin cewa, APC ta dakatar da Orji Kalu ne saboda cin dunduniyar jam'iyyar.
A cewar sanarwar da aka fitar:
"An dakatar da shi ne bayan bincike mai zurfi da shawarin kwamitin ladabtarwa da gundumar Igbere, karamar hukumar Bende da kuma shugabannin jam'iyyar.
"Ku sani cewa jam'iyyar ta damu da mutuncinta saboda haka ba zata lamunci wani zagon kasa ba."
Asali: Legit.ng