Hukumar EFCC Ta Cafke N32.4m Na Siyan Ƙuri'a a Jihar Legas

Hukumar EFCC Ta Cafke N32.4m Na Siyan Ƙuri'a a Jihar Legas

  • Hukumar EFCC ta samu wata gagarumar nasara, ta cafke wasu maƙudan kuɗaɗe a jihar Legas
  • Hukumar tayi zargin cewa maƙudan kuɗaɗen da ta cafke za ayi amfani ne da su a wajen siyan ƙuri'a a zaɓen gobe
  • Ana zargin cewa zaɓen da za a gudanar gobe a Najeriya za ayi amfani da kuɗi domin siyan ƙuri'a

Legas- Hukumar hana cin hanci da rashawa ta ƙasa (EFCC) ta samu nasarar cafke wasu maƙudan kuɗaɗe da aka yi niyyar siyan ƙuri'a da su a jihar Legas.

Hukumar ta EFCC ta cafke naira miliyan talatin da biyu da dubu ɗari huɗu waɗanda ake zargin za a yi amfani da su wajen siyan ƙuri'a a jihar Legas.

Hukumar EFCC
Hukumar EFCC Ta Cafke N32.4m Na Siyan Ƙuri'a a Jihar Legas Hoto: Facebook/EFCC
Asali: Facebook

Hukumar EFCC shiyyar jihar Legas ta sanar da cewa tuni aka tasa ƙeyar wanda ake zargin domin amsa tambayoyi.

Kara karanta wannan

2023: Jerin Wasu Muhimman Abubuwa 5 Da Zasu Taka Muhimmiyar Rawa a Zaɓen Shugaban Ƙasa

Sai dai hukumar ba tayi ƙarin haske ba kan sunan wanda aka cafken da kuma wacce jam'iyya yake yiwa aiki.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cikin ƴan kwanakin nan dama hukumar tace zata sanya ido sosai akan ɓata garin da zasu fito da kuɗi domin siyan ƙuri'a a zaɓukan da za a gudanar a ƙasar nan.

Shugaban hukumar na ƙasa, Abdulrasheed Bawa, yayi kira ga jami'an hukumar da aka tura sanya ido lokacin zaɓe, da kada su yarda ɓata su ƙaƙata sahihancin zaɓen ta hanyar yin amfani da kuɗi.

Tuni dai hukumar ta baza jami'an ta ko ina a faɗin ƙasar nan domin sanya ido sosai akan zaɓen.

Ana tunanin cewa halin ƙarancin kuɗi ka iya bada ƙofa da ɓata gari za suyi amfani da ita domin siyan ƙuri'a a zaɓen.

Wasu Abubuwa Biyar Da Zasu Taka Rawar Gani a Zaɓen Gobe

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari Yayi Allah Wadai Da Kisan Ɗan Takara Ana Dab Da Zaɓe, Ya Ba Jami'an Tsaro Wani Umurni

A wani labarin na daban kuma, wata cibiya tayi nazari kan wasu muhimman abubuwa guda biyar waɗanda za su taka muhimmiyar rawa a zaɓen shugaɓa ƙasa na Najeriya, wanda zai gudana a goɓe Asabar.

Cibiyar ta tsaya ta natsu tayi bayani filla-fillan kan yadda abubuwan za su taka rawa a zaɓen na Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng