Dalilin Da Ya Sanya Ba Zamu Iya Kama Gwamnoni Ba Kan Sauya Fasalin Kuɗi, IGP

Dalilin Da Ya Sanya Ba Zamu Iya Kama Gwamnoni Ba Kan Sauya Fasalin Kuɗi, IGP

  • Shugaban hukumar ƴan sandan Najeriya yayi ƙarin haske kan dalilin da ya sanya hukumar bata tuhumi gwamnonin dake adawa da sauya fasalin takardun kuɗi ba
  • Ana dai ganin gwamnoni na yin kalamai waɗanda basu kamata ba a kan sauya fasalin takardun kuɗin
  • Shugaban ya bayyana abinda hukumar ƴan sanda zata yiwa gwamnonin masu yin waɗannan kalaman

Abuja- Shugaban hukumar ƴan sandan Najeriya, IGP Usman Baba, yace ba zasu iya tuhumar gwamnoni ba bisa kalaman da suke yi na rura wuta kan shirin sauya fasalin takardun kuɗin naira na babban bankin Najeriya (CBN)

Usman Baba yayi magana ne da ƴan jarida bayan kammala taron hukumomin tsaron ƙasa wanda shugaba Buhari ya jagoranta. Rahoton The Cable

Usman Baba
Dalilin Da Ya Sanya Ba Zamu Iya Tuhumar Gwamnoni Ba Kan Sauya Fasalin Kuɗi, IGP Hoto: The Cable
Asali: UGC

Gwamnoni irin su Nasir El-Rufai na jihar Kaduna da Dapo Abiodun na jihar Ogun, sun fito fili sun yi fatali da umurnin shugaba Buhari kan sauya fasalin takardun kuɗin.

Kara karanta wannan

Magana Ta Fito: Dalilan da Suka Sa EFCC Ba Ta Damke Ko Mutum Ɗaya Ba Kan Karancin Naira

Da yake magana kan kalaman da gwamnonin suka yi waɗansa wasu ke yiwa kallon 'kalaman rura wuta', yace ba za a iya tuhumar gwamnonin da aka samu suna aikata hakan ba saboda suna da rigar kariya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yayi nuni da cewa duk da rigar kariyan da gwamnonin suke da ita, hukumar ƴan sanda zata aike da jan kunne zuwa gare su domin su kiyayi yin irin waɗannan kalaman. Rahoton Premium Times

“Dukkanin mu mun san dalilin da ya sanya ba za a iya tuhumar su ba. Muna gudanar da bincike. Duk wanda yayi wani abu za a iya bincikar sa." A cewar sa
"Amma domin yin tuhuma, akwai wasu mutane da suke da rigar kariya. Ina tunanin wannan na ɗaya daga cikin dalilan, amma hakan ba zai hana mu mu jan kunnen su ba, daga gargaɗin su ba, da basu shawara ba, kuma muna yin hakan."

Kara karanta wannan

Wahala Ta Kare: An Fara Zuwa Gida-Gida Rabawa Mutane Sabbin Kuɗi a Jihar Kano

Abinda Yasa Har Yanzu Bamu Kama Kowa Kan Karancin Naira Ba, EFCC

A wani labarin na daban kuma, hukumar EFCC ta bayyana dalilin da ya sanya bata cafke kowa ba kan ƙarancin sababbin takardun naira ba.

Shugaban hukumar na ƙasa, Abdulrashid Bawa, shine ya bayyana dalilan da ya sanya hukumar ba tayi ram da kowa ba har ya zuwa yanzu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng