Gwamnatin Kogi Tayi Alla-Wadai Da EFCC Bayan Kwace Wasu Kadarorin Gwamna Yahaya Da Kotu Tayi

Gwamnatin Kogi Tayi Alla-Wadai Da EFCC Bayan Kwace Wasu Kadarorin Gwamna Yahaya Da Kotu Tayi

  • Gwamnatin Kogi ta mayar da martani mai zafi kan hukuncin da babbar kotun tarayya ta yanke
  • Gwamnatin jihar ta yi zafafan kalamai kan shugaban hukumar yakida rashawa EFCC, AbdulRashid Bawa
  • Kotu dai ta umurci EFCC ta wallafa wadannan kadarori a jaridu nan da kwanaki 14 masu zuwa

Lokoja - Gwamnatin jihar Kogi ta yi Alla-wadai da Shugaban hukumar hana almundahana da yaki da rashawa EFCC, AbdulRashid Bawa, bisa hukuncin da kotu ta yanke ranar Laraba.

Gwamnatin ta ce AbdulRasheed Bawa da iyayen gidansa na fito-na-fito da ita kuma zai ji kunya, rahoton ThisDay.

Legit Hausa a ranar Laraba, 22 ga wata cewa babban kotun tarayya dake Legas ta baiwa EFCC izinin mallake wasu manyan kadarorin da ake zargin na gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ne.

Wadannan dukiyoyi sun hada da gidaje a Abuja, Legas da kasar Dubai.

Kara karanta wannan

Da Dumi: Kotu Ta Amincewa Gwamnati Kwace Wasu Kadarori 14 Da Ake Zargin na Gwamnan Kogi ne

EFCCC
Jami'an EFCC, Hukumar Ta Kwace Wasu Kadarorin Gwamna Yahaya Hoto: EFCC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kwamishanan labarai da sadarwa na jihar Kogi, Kingsley Fanwo, a jawabin da ya fitar ranar Laraba ya bayyana cewa Bawa ya lashi takobin yakar duk wanda dauka matsayin makiyi maimakon mayar da hankali kan aikinsa.

Yace gaba daya jami'an hukumar EFCC marasa tunani ne tun da har zasu rika alakanta gwamnatin jihar da wadannan kadarori, riwayar AriseTV.

A cewarsa. gwamnatin jihar Kogi ba tada wasu kadarori cikin wadananna da ake bincike, kawai bita da kulli ake mata.

Ya ce shugaban EFCC yana kokarin fito-na-fito da jihar Kogi saboda Gwamnan jihar, Yahaya Bello na biyayya ga jam'iyyar All Progressives Congress maimakon wasu daidaikun miyagu.

A cewarsa:

"Yan Najeriya da duniya gaba daya ba jahilai bane kamar Bawa da masu daukar nauyinsa. Suna sane da bita da kullin da ake yiwa gwamnatin jihar Kogi da jami'anta. Kowa ya sani cewa yanzu EFCC ta zama hedkwatar rashawa karkashin Bawa."

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Gwamnan Jihar Rivers Ya Shiga Karar Gwamnoni Da Buhari Kan Naira A Kotun Koli

"Muna san bayyanawa duniya cewa, bisa abubuwan da muka gani a kafafen yada labarai, lamarin mallake kadarori na da tsari wanda zai baiwa duk mammallakin dukiyar ya fito yayi da'awa. Zamu bi tsarin kotu."
"Zamu nunawa kowa cewa muna da gaskiya a kotu. Komai lokaci ne."

Hukuncin kotu na Laraba

Kotu ta ce gwamnatin tarayya da mallake wadannan dukiyoyi na wucin gadi kuma ta wallafa hotunansu a jaridu nan da kwanaki 14 don duk wanda ya san nashi ne ya gabato.

EFCC ta ce wadannan kadarori na da alaka da gwamnatin jihar Kogi da gwamnanta.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida