Ku Dage Ku Zabi Tinubu a Zaben Bana, APC Ta Roki ’Yan Najeriya Alfarma
- Jam’iyyar APC ta ce wannan ne daman ‘yan Najeriya, su zabi Bola Ahmad Tinubu a zaben 2023 da ke a ranar Asabar mai zuwa
- Wannan na fitowa ne daga bakin wani jigon jam’iyyar a lokacin da yake zantawa da manema labarai a birnin Akura, jihar Ondo
- Ya kuma bayyana cewa, da zarar an zabi Tinubu, to komai na wahala da kasar nan ke fuskanta zai zama tarihi
Jihar Ondo - Jam’iyyar APC mai mulki ta shawarci ‘yan Najeriya da su kasance masu jajircewa kana su dage su zabi Bola Ahmed Tinubu a zaben shugaban kasa da ke tafe nan ba da jimawa ba.
Wannan na zuwa ne daidai lokacin da kasar ke ci gaba da fuskantar karancin sabbin Naira ga kuma kuncin wahalar layi a banki na neman kudade.
Jam’iyyar ta bayyana kwarin gwiwar cewa, halin kunci da kasar ke ciki zai kau nan kusa idan aka zabi Tinubu ya gaji Buhari a zaben ranar Asabar mai zuwa.
Wannan batu na fitowa ne daga bakin mataimakin shugaban jam’iyyar APC na kasa daga shiyyar Kudu maso Yamma, Mr. Isaack Kekemeke, Punch ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wahalar kudi, man fetur duk za su zama tarihi, inji jigon APC Mr. Isaac
A cewarsa, karancin kudi, wahalar man fetur da tsadarsa da kuma sauran kalubalen kasar duk masu wucewa ne nan ba da jimawa ba.
Ya kuma yi nuni da cewa, Tinubu ya magantu da masu kada kuri’u a yankuna daban-daban na kasar, inda yace yana da shirye-shiryen kai Najeriya ga tudun tsira, haka nan Punch ta ruwairo.
Ya kuma mika godiya ga dukkan dubatan ‘yan Najeriya da ke nuna kauna ga Tinubu a duk inda ya taka a kasar nan da sunan kamfen takarar shugaban kasa da yake yi.
Atiku za mu zaba a zaben 2023
A wani labarin kuma, kun ji yadda kungiyar ‘yan Arewa ta ce ta gamsu da takarar Alhaji Atiku Abubakar a zaben da ke take nan da ranar Asabar 25 ga watan Faburairu.
Jigon ACF ya bayyana cewa, tuni wasu manyan Arewa suka bayyana goyon bayansu ga dan takarar shugaban kasa na PDP a zaben bana saboda wasu dalilai.
Ba wannan ne karon farko da wata kungiya ke fitowa ta bayyana goyon baya ga dan takarar shugaban kasa na PDP ba.
Asali: Legit.ng