Matashi Ya Baje Kolin Tsabar Kudin Da Ya Shafe Shekaru Yana Tarawa a Gida
- Wani matashi dan Najeriya ya garzaya soshiyal midiya don baje kolin kudaden da ya dauki shekaru biyu yana tarawa a gida
- A cewarsa, kudirinsa shine ya ci gaba da ajiyar kudi haka har zuwa shekaru hudu ko biyar masu zuwa idan ba don sauya kudi da CBN ta yi ba
- Masu amfani da soshiyal midiya sun nuna mamaki da ganin tarin kudaden da ya fito da su daga asusun yayin da yake godiya ga Allah
Cike da farin ciki, wani dan Najeriya mai suna Jimoh ya baje kolin kudaden da ya dauki tsawon lokaci yana tarawa a gida.
Jimoh ya fasa asusun bankinsa na katako sannan ya fito da kudaden yan naira dubu-dubu yayin da yake godiya ga Allah a kan wannan ni'ima da ya yi masa na samun damar tara kudi.
Yayin da yake alfahari da wannan namijin kokari da ya yi, Jimoh ya ce sai mutum ya daure kafin ya iya tara kudi kuma ya bayyana cewa ya tara kudin ne tsawon shekaru biyu.
Jimoh ya ce ya fara tara kudi a cikin asusun tun a ranar 19 ga watan Janairun 2023 kuma ya fito da kudin a watan Janairun 2023.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Da yake bayyana nasarar da ya samu a TikTok, ya rubuta:
"Na fara tara kudi a ranar 19 ga watan Janairun 2021, idan ba don CBN ba na so na dauki shekaru 4-5 ina tara kudi."
Kalli bidiyon a kasa:
Jama'a sun yi martani
Gracious ta ce:
"Da zai fi ka zuba jari a kan fili, da ya kjara daraja zuwa yanzu."
YOUR BABE BESTIE Danny ta ce:
"Ka yi addu'a Allah ya sa banki su karba."
Mr. Jumboya ce:
"Bai da amfani tara kudi a naira zai fi ka tara shi a dala amma ba dala ba, abun da za ka iya siya da N1000 a 2021 ba zai siyu ba a yanzu."
A wani labarin kuma an yi nasarar damke wani matashi wanda aka gani da bandir-bandir din kudi yan N500 amma na bogi.
Yan sanda sun tabbatar da lamarin inda suka bazama gudanar da bincike don gano gaskiyar abun da ke kewaye da lamarin
Asali: Legit.ng