Saura ‘Yan Kwanaki Gwamnati ta Kare, Buhari Ya Karbo Bashin Naira Tiriliyan 2.1

Saura ‘Yan Kwanaki Gwamnati ta Kare, Buhari Ya Karbo Bashin Naira Tiriliyan 2.1

  • Bashin da gwamnatin tarayya ta karbo daga hannun kamfanonin gida ya kai Naira tirilyan 2.13
  • Shugaba Muhammadu Buhari yana cigaba da cin bashi, alhali zai bar mulki gwamnati a Mayu
  • Fiye da 85% na harajin da gwamnati take iya tatsowa a 2023, yana tafiya ne a wajen biyan bashi

Abuja - A wannan sabuwar shekara ta 2023 da aka shiga, kimanin Naira tirilyan 2.13 gwamnatin tarayya ta karbo a matsayin bashi a nan cikin gida.

Wani bincike da jaridar The Nation ta gudanar, ya nuna gwamnati ta dage wajen karbo bashi a lokacin da wa’adin gwamnati mai-ci ya zo karshe.

Alkaluma sun nuna cin bashin da Shugaba Muhammadu Buhari yake yi, ya karu.

Bayanan da aka samu ya nuna tsakanin Junairu zuwa Fubrairun 2023, gwamnatin Najeriya ta iya tattaro Naira Tiriliyan 2.129 ta hanyar karbo aro.

Kara karanta wannan

Bayan Jawabin Buhari, CBN Ya Aike da Muhimmin Sako Ga Yan Najeriya, Ya Faɗi Abu 3 Kan Sabbin Naira

A yadda ake tafiya, rahoton ya bayyana gwamnati za ta iya zarce Naira Tiriliyan 7.04 da aka yi nufin za a karbo bashi a cikin gida a shekarar bana.

Buhari
Shugaba Buhari a Addis Ababa Hoto: @BashirAhmaad
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ganin an soma sa ido a kan yadda ake cin bashi daga kasashe da kamfanonin ketare, da-alama gwamnatin kasar nan ta fara karkatar da kokonta.

Idan aka yi bayani dalla-dalla, gwamnati ta iya samun Naira tiriyan 1.189 a watan Fubrairun nan, hakan ya zarce abin da aka samu a Junairu da 26%.

A Junairu an samu Naira biliyan 940.62 ne wanda Naira biliyan 277.468 suka fito daga tsarin NTBs sai kuma Naira miliyan 533 a karkashin FGNSBs.

A watan nan kuwa, Naira biliyan 417.04 aka samu daga NTB, sai Naira biliyan 1.271 ta FGNSBs.

Bashi zai kai N45tr a 2023

Har zuwa karshen 2022, bashin da ake bin kasar Naira tiriliyan 44.06 ne. Haka zalika ana shirin sake karbo bashin Naira tiriliyan 10.78 shekarar nan.

Kara karanta wannan

Karancin Kudi: Gwamna Ya Samar Da Bas Din Kyauta Don Ragewa Al'ummarsa Radadin Halin Da Ake Ciki

Daga karshen 2022 zuwa yanzu, rahoton ya nuna an samu karin 50% a bashin da ake karbowa, a yau bashi na cinye kusan 85% na kudin shigar gwamnati.

Kyau a kama El-Rufai - Hon.

Rahoto ya zo cewa Hon. Samaila Suleiman wanda shi ne ‘Dan majalisa mai wakiltar Kaduna ta Arewa, ya ja hankalin hukuma a kan gwamnan Kaduna.

Hon. Suleiman ya nuna ya kamata Jami’an tsaro su damke Malam Nasir El-Rufai da zarar ya bar karagar mulki saboda ya halatta kashe tsofaffin kudi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng