Gwamnoni 10 Sun Sake Maka Buhari Kotu, Sun Bukaci A Soke Umurninsa Kan N200, Jerinsu
Jihohi goma sun bukaci kotun koli ta soke umurnin Shugaba Muhammadu Buhari kan dawo da tsaffin N200 kadai ba tare da N500 da N1000.
Sun sanar da kotun cewa wannan ya sabawa kundin tsarin mulkin Najeriya.
Zaku tuna cewa a ranar Alhamis, 16 ga Febraiaru, Buhari ya umurci CBN ya fito da tsaffin takardun N200.
Hakan ya biyo bayan umurnin kotun koli cewa a cigaba da amfani da tsaffin N200, N500 da N1000.
Gwamnatocin jihar a sabon karar da suka shigar sun bukaci kotu tayi watsi da umurnin Shugaba Buhari.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Gwamnonin sun bukaci kotun ta sanar da cewa har yanzu halal ne amfani da tsaffin N200, N500 da N1000.
Jihohin sun hada da:
1. Kaduna
2. Kogi
3. Zamfara
4. Ekiti
5. Ondo
6. Katsina
7. Ogun
8. Cross Rivers
9. Legas
10. Sokoto
A karar da suka shugar, jihohin sun bayyana cewa Shugaban kasa ya bada wani umurni da yaci karo da na kotun koli/
A cewar karar:
"Sabanin umurnin wannan kotun mai girma, wanda aka shigar da kara na farko ta bakin shugaban kasa da bankin tarayya CBN sun saki jawabai cewa a haramta amfani da tsaffin kudi, kuma hakan ya jefa jama'a cikin rudani kan umurnin da za'a bi."
"Wanda ake kara na farko ya saba umurnin wannan kotu da gayya ranar Alhamis, 16 ga Febrairu 2023 lokacin da Shugaban kasa ya gabatar da jawabi ga al'ummar Najeriya, lokacin da Shugaban kasa ya yi kalaman da suka saba umurnin kotu karara inda yayi umurnin cewa a daina amfani da dukkan tsafin kudi illa N200 kuma babu bankunan da zasu karbi wannan kudi sai CBN."
Saura mako daya zabe: Jam'iyyar APC tayi shelar zaman gaggawa da gwamnoni
Kun ji labarin cewa Uwar Jam'iyyar All Progressives Congress APC ta kira zaman gaggawa da gwamnonin jam'iyyar yayinda ake sauran mako guda zaben shugaban kasa.
Zaben shugaban kasa da yan majalisar dokokin tarayya zai gudana ranar 25 ga watan Febrairu, 2023.
Shugaban uwar jam'iyyar, Abdullahi Adamu, ne ya kira zaman kuma Sakataren yada labaran jam'iyyar, Felix Morka ya sanar.
Asali: Legit.ng