A Kodayaushe Na Kan Fada Masa Kada Ya Mutu Kafin Ni: TY Danjuma Na Alhinin Mutuwar Amininsa
- Tsohon shugaban ma'aikatan tsaron Najeriya ya bayyana cewa ya so ace shi ya mutu kafin amininsa
- Theophilus Danjuma ya bayyana haka a wajen taron jinjina da bankwana ga tsohon jakadan Najeriya a Rasha Dan Suleiman
- A cewar Danjuma, bisa al'ada, shi ya kamata ace abokinsa kuma kaninsa ya binne ba wai akasin haka ba
Theophilus Danjuma, tsohon shugaban ma'aikatan tsaro ya nuna bakin cikinsa a kan mutuwar tsohon jakadan Najeriya a Rasha, Air Commodore Dan Suleiman.
Jaridar Punch ta rahoto cewa Danjuma wanda ya yi bankwana da Suleiman a wani taron jinjina da wakoki wanda ya samu halartan sauran shugabanni a Abuja ya bayyana marigayin a masayin amini wanda ya cancanta.
Suleiman, dan kishin kasa kuma daya daga cikin shugabannin kungiyar arewa ta tsakiya kuma yan mazan jiya ya mutu a ranar 1 ga watan Fabrairu.
Don Suleiman mutumin kirki ne, TY Danjuma
Da yake magana a taron a Abuja, Danjuma ya ce ya shiga damuwa matuka a kan rasuwar Suleiman, rahoton Blueprint.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Kalamansa:
"Dan ya fi ni karancin shekaru. Ni dan gargajiya ne kuma bisa al'adana, shi ya kamata ya binne ni, ba wai ni na binne shi ba.
"Bai kamata na kasance a nan ba, saboda ya zama dole ba za a yi ba ni ba saboda ya kasance mutumin kirki.
"A kullun ina fada mashi kada ya mutu kafin ni, amma hakan ce ta faru. Don haka na yanke shawarar bayyana a nan sannan na yi magana da iyalinsa a sirrince kafin na koma Lagas inda nake da zama.
"Wasu da suka yi magana kafin ne sun yi zantukan bankwana masu ban mamaki ga Daniel kuma babu abun da zan kara."
An gano bidiyon tsohuwa mai shekaru 150 a duniya a Najeriya
A wani labarin, bidiyon wata tsohuwa yar Najeriya da ake kyautata zaton ta kai shekaru 150 a duniya ya bayyana kuma ya matukar ba mutane mamaki.
Duk da yawan shekaru da tsufar matar tana cikin yanayi mai kyau domin dai fatar jikinta sai sheki da walwali ke yi kuma ya nuna lallai an sha kyau ba kadan ba a lokacin kuruciya.
Wata mai aikin taimako ce ta ziyarci matar bayan samun labarinta inda ta kai mata kayan abinci a yanzu da ake fama da rashin wadatar kudi.
Asali: Legit.ng