Saudiyya, Iran Da Wasu Kasashe 3 Da Basa Raya Ranar Masoya Ta Duniya

Saudiyya, Iran Da Wasu Kasashe 3 Da Basa Raya Ranar Masoya Ta Duniya

Kamar yadda muka sani an dade da ware ranar 14 ga watan Fabrairun kowace shekara a matsayin ranar masoya ta duniya. A kasashen duniya da dama, mutane na bai wa wannan rana muhimmanci inda sukan kasance tare da masoyansu tare da yi masu kyaututtuka.

Sai dai kuma wasu yan adadi na kasashen Yamma basa raya wannan rana ta masoya wato 'Valentine' saboda bambancin addinansu.

Ranar masoya
Saudiyya, Iran Da Wasu Kasashe 3 Da Basa Raya Ranar Masoya Ta Duniya Hoto: NBC News
Asali: UGC

Ga jerin kasashen da ba sa bikin ranar masoya:

1. Uzbekistan

Uzbekistan kasa ce mai daddiyar tarihi da al'adu iri-iri kuma yawancin yan kasar mabiya addinin Islama ne.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kasar ta yarda da bikin ranar masoya ta duniya har sai a 2012 lokacin da sashen fadakarwa da inganta dabi'u na ma'aikatar ilimin kasar ya kafa wata doka da ya haramta raya wannan rana.

Kara karanta wannan

Bidiyon Matashin Najeriya da ya auri BaIndiya, Yace Burinsa a Rayuwa ya Cika

Maimakon gudanar da bikin 'Valentine', mutanen Uzbekistan kan yi murnar zagayowar ranar haihuwar jarumin kasar Babur, wanda ya kasance sarkin Mughal. Ranar masoya ta duniya ba haramun bane amma dai ba'a karfafa shi ba don karrama bikin tunawa da Babur.

2. Iran

A shekarun baya, hukumomin kasar Iran sun yi nufin haramta bikin ranar masoya, inda suka ce ranar tana yada miyagun dabi'un yammacin duniya sannan suka yi barazanar hukunta shaguna da gidajen cin abinci idan suka siyar da kyaututtukan ranar masoya.

Duk da haka, an rahoto cewa an karbi hayan gidajen cin abinci da dama a Tehran sannan an gano shaguna da dama suna siyar da bebin yar-tsana da cakulet.

Kasancewar suna karya doka ne, wuraren na amfani da masu bincike don ganin ko jami'an tsaron na sintiri na ranar masoya.

3. Indonesia

Magana ta gaskiya, babu wata doka ta fito ta haramta bikin ranar masoya a Indonesia. Sai dai kuma a wasu yankunan kasar kamar su Surabaya da Makassar inda ake da yawan Musulmai ana dan saka takunkumi kadan yayin da a Bando Aceh, an haramta bikin.

Kara karanta wannan

Ba Zan Tashi a Tutar Babu Ba: Uwar Biki Ta Fito Da Lambar Akant a Wurin Liyafar Bikinta, Ta Ce kowa ya Tura Mata Kudi

4. Saudi Arabia

A kasar Saudiyya, jami'an tsaro na Hisba sun haramta bikin na ranar Masoya. An haramta siyar da furanni, jajjayen abubuwa da katuna masu dauke da zantukan soyayya don shirin ranar 14 ga watan Fabrairu. Hakan ya haifar da kafa kasuwar bayan fage na kayan 'Valatine'.

5. Malaysia

Malaysia kasa ce ta tarayya kuma kundin tsarin mulkin kasar ya ba kowa damar yin addininsa, sai dai kuma kasa ce mai kabilu da al’adu daban-daban, wanda kimanin kaso 60 na al'ummarta Musulmai ne. Babbar birnin kasar ita ce Kuala Lumpur.

Tun a 2005, aka haramta bikin ranar masoya. Sashin ci gaban Musulunci na kasar Malaysia ya ce bikin ranar na bayar da damar aikata masha'a kama daga zubar da ciki, shan giya sannan ta riki cewa wannan na iya haifar da annoba da lalata dabi'u a tsakanin matasa.

Akwai ma kamfen da akan yi duk shekara don yin adamawa da ranar masoyan don karfafa wannan hange. Duk wanda ya fita don raya wannan rana toh yana cikin hatsari, ciki harda na kamu.

Kara karanta wannan

Matasa Sun Kwato Wani Matashi Karfi Da Yaji Hannun Yan Sanda Kan Batanci ga Al-Qur'ani, Sun Kasheshi

Babu kunya: Budurwa ta yi bikin zagayowar ranar haihuwar mahaifinta mai tabin hankali

A wani labarin, wata matashiyar budurwa ta cire kunya ta taya mahaifinta mai lalurar tabin hankali murnar zagayowar ranar haihuwarsa inda ta saki bidiyonsu a tare cikin farin ciki da annashuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng