Miyagun Yan Bindiga Sun Bankawa Babbar Kotun Jihar Imo Wuta
- 'Yan bindigan da ba'a san su waye ba sun ƙona babbar kotun Oguta mai zama a ƙaramar hukumar Oguta, jihar Imo
- Wata majiya ta bayyana cewa maharan sun lalata manyan Ofisoshin kotun yayin harin na daren jiya Lahadi
- Wannan na zuwa ne kwanaki 10 kacal bayan harin da ya yi Ajalin Alƙali ana tsaka da shari'a a jihar kudu maso gabas
Imo - Wasu tsagerun 'yan bindiga sun ƙone babbar Kotun Oguta, mai zama a karamar hukumar Oguta, jihar Imo da ke kudu maso gabashin Najeriya.
Punch ta tattaro cewa maharan sun isa wurin da misalin ƙarfe 11:30 na daren ranar Lahadi kana suka aikata ta'adi a Kotun wacce ke cikin hedkwatar ƙaramar hukumar.
Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta saboda dalilan tsaro ta bayyana mummunar ɓarnar da maharan suka yi da muhimman ofishin da suka ƙone.
A cewar majiyar Ofishin rijista na Kotun majistire, ofishin adana bayanan Kotun ɗaukaka kara,, ɗakin ajuye fayil-fayil, ofishin Sakataren alƙalin babbar kotu, harabar babbar Kotun jiha duk sun kone a harin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majiyar ta ce:
Ofishin rijista na Kotun majistire, ofishin adana bayanan Kotun ɗaukaka kara,, ɗakin ajuye fayil-fayil, ofishin Sakataren alƙalin babbar kotu da Ofishin beli dun sun ƙone kurmus yayin da wani sashi na harabar cikin Kotun ya ƙone."
"Kusan baki ɗaya ginin babbar Kotun ya yi kaca-kaca, babu wani mutum mai hankali da zai uya tunkaɗar wurin."
Shugaba mai rike da ƙaramar hukumar Oguta, Ofili Ijioma, ya ce tuni suka sanar da hukumomin tsaro abinda ya faru.
Haka zalika ya tabbatarwa wakilin jaridar Daily Trust cewa za'a gudanar da bincike na musamman wanda zai tona asirin waɗanda suka aikata wannan ta'adi.
Wannan harin na zuwa ne kwanaki 10 bayan wasu maharan sun kashe Alkalin Kotun Kwastumare mai zama a Ejemekwuru, Nnaemeka Ugboma, tana tsaka da zaman shari'a.
Yan Bindiga Sun Harbi Shugaban PDP Na Gunduma
A wani labarin kuma Wasu tsagerun mahara sun shiga har cikin gida sun harbi shugaban PDP a jihar Imo
Rahotanni sun ce ɗan siyasan ya shiga gida da misalin ƙarfe 9:00 na daren ranar Asabar ba tare da sanin maharan sun masa kwantan ɓauna ba.
Tuni dai aka garzaya da shi Asibiti domin kula da lafiyarsa yayin da jami'an tsaro suka fara binciken gano waɗanda suka kitsa harin.
Asali: Legit.ng