Buhari ya Isa Hedkwatar Tsaro Don Aiwatar da Muhimmin Aiki Kafin Zabe

Buhari ya Isa Hedkwatar Tsaro Don Aiwatar da Muhimmin Aiki Kafin Zabe

  • Shugaban kasan Najeriya, Muhammadu Buhari, ya halarci kaddamar da wasu kayayyakin aiki a hedkwatar 'yan sandan Najeriya
  • Wannan na zuwa ne kasa da kwanaki 12 kafin zabe inda rundunar ta samu ababen hawa, da sauran kayan aiki don zabe mai zuwa
  • Shugaban kasan ya yabawa Sifeta Janar na 'yan sandan Najeriya kan kokari, jajircewa da zamanantar da aikin 'yan sandan

FCT, Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa hedkwatar tsaro domin kaddamar da kayayyakin aiki na ‘yan sanda.

Muhammadu Buhari
Buhari ya Isa Hedkwatar Tsaro Don Aiwatar da Muhimmin Aiki Kafin Zabe. Hoto daga thenationonlineng.com
Asali: UGC

Buhari ya dira wurin karfe 10:15 na safe tare da manyan jami’an gwamnati.

Shugaban kasan Najeriya, Muhammadu Buhari, GCFR, ya halarci hedkwatar tsaro ta 'yan sandan Najeriya da ke gidan Louis Edet a Abuja a ranar Litinin, 13 ga watan Fabrairun 2023.

Ya kaddamar da tarin kayan aiki da rundunar 'yan sandan Najeriyan ta siya don inganta ayyukan hukumar balle a zaben 2023 mai zuwa.

Kara karanta wannan

Tsautsayi: 'Yan sanda sun dauki mataki kan faston da aka ga ya rataye AK-47 a Abuja

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kayayyakin da suka hada da ababen hawa na aiki, kayan shawo kan taro da ababen tarwatsa zanga-zanga. Akwai kwamfuyutoci da aka siyo domin tabbatar da an bi dokokin zabe yayin zaben da ke zuwa.

A wallafar da rundunar tayi a shafinta na Twitter, duk wannan tanadin an yi su ne domin zabe mai zuwa da kuma tabbatar da karfin ingancin aikin rundunar 'yan sandan Najeriyan.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yabawa kokarin sifeta janar na 'yan sandan Najeriya wurin kokarin shugabancinsa na gyarawa, zamananatarwa da zaburar da jami'an 'yan sanda kan gogewa da mutunta dokokin aikinsu.

Jama'a sun firgice a Binuwai kan shawagin helikwafta

A wani labari na daban, jama'ar jihar Binuwai mazauna yankin Onyagede sun koka kan tsoro da firgici da suka fada sakamakon shawagin wani helikwafta a karamar hukumar Ohimini a jihar.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Gwamnan CBN ya yi wata ganawar sirri da Buhari kan batun Naira

Sun tabbatar da cewa, helikwaftan yana ta sauke wasu irin sojoji da ke bayyana a mitsike kuma wani tsohon soja mazaunin yankin ya tabbatar ba sojoji bane.

Sai dai gwamnatin jihar ta sanar da cewa, jirgin saman mallakin wani kamfanin hakar kwal ne kuma da shi ake amfani.

Wasu jama'ar yankin sun ce hatta a ranar Juma'a da ta gabata, an sauke mutanen har sau wurin uku a yankin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng