Wani Dan Najeriya Ya Zama Lakcaran Malamarsa Ta Ajin 'Nursery', Hotunan Masu Kyau

Wani Dan Najeriya Ya Zama Lakcaran Malamarsa Ta Ajin 'Nursery', Hotunan Masu Kyau

  • Wani Lakcara ya sha mamaki lokacin da ya shiga aji ya tarar daya cikin dalibansa tsohuwar malamarsa ce
  • Mutumin mai suna Anucha Wisdom yana koyarwa ne a Tsangayar Ilimi ta Jami'ar Jihar Abia inda a yanzu tsohuwar malamarsa ta ke matsayin daliba
  • Ya wallafa hotunan lokacin da suka hadu da yadda ya tsuguna ya gaishe ta cike da farin ciki da girmamawa

Wani dan Najeriya ya zama lakcaran malaman da ta koyar da shi a makarantar nursery.

Lakcaran mai suna Anucha Wisdom yana koyarwa ne a Tsangayar Ilimi na Jami'ar Jihar Abia, Uturu.

Anucha Wisdom
Wani Dan Najeriya Ya Zama Lakcaran Malamarsa Ta Nursery, Hotunan Masu Kyau. Hoto: Anucha Wisdom
Asali: Facebook

A wani wallafa da ya bazu a Facebook, Anucha ya ce bai taba sani cewa malamarsa na nursery mai suna Aunty Ijeoma ta zama daliba a jami'ar na ABSU ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Zance ya fito: Bayan Ganawar Tinubu Da Dangote Da Matawalle, Batutuwa Sun Fito Waje

Hotunan mutumin da ya zama lakcaran malamarsa ta nursery 3 a ABSU

Anucha ya ce ya shiga aji kawai sai ya gano Aunty Ijeoma tana daya cikin daliban da ke yin darasin da ya ke koyarwa.

Ya cika da murna a yayin da suka rungume juna. Ya bayyana malamar a matsayin mai mutunci da kirki sosai.

Anucha ya ce a Facebook:

"A farkon satin nan, na hadu da Aunty Ijeoma, wacce ta koyar da ni a nursery 3 a makarantar St. Joseph Development Nursery/Primary School Umuchichi Aba. Ashe a sashin da na ke koyarwa ta ke kuma ban sani ba, har sai ranar da ta zo yin darasin da na ke koyarwa.
"Aunty, na gode saboda koyar da ni da kyau da kika yi. Na zama abin da na zama yau ne saboda kin koyar da ni da kyau. Lallai rayuwa duk abin da ka yi zai dawo."

Kara karanta wannan

Har Yanzu Peter Obi Ya Fi Tinubu, Atiku Da Saura, In Ji Obasanjo, Ya Bada Dalili

Martani daga masu amfani da Facebook

David Mbagwu ya ce:

"Dan uwa, kowa na bukatar ya karanta wannan ya hankaltu. Na sha fada wa lakcarorin da ke kusa da ni, ya kamata su zama masu hikima kada su yi tunanin al'amura ba za su iya canja wa ba. Allah ya yi wa Aunty IJ albarka."

Stanley Ayu:

"Wannan abin karfafa gwiwa ne. Lallai akwai abubuwan mamaki a gaba. Allah ya kara mama daukaka a sabon abin da ka sa a gaba."

Babban malamin jami'an Nasarawa Da Yaransa Sun Lakada Wa Wata Daliba Duka Don Ta Yi Rikici Da Yarsa Kan Saurayi

A baya mun kawo muku cewa yan sanda sun kama wani lakcara a Jami'ar Jihar Nasarawa, Fred Ekpe Ayokhai, PhD, saboda cin mutuncin wata daliba wacce ta yi rikici da yarsa kan wani saurayi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: